18 Maris 2026 - 17:05
Source: ABNA24
Iran Ta Gargaɗi Jama'ar Da Ke Kusa Da Cibiyoyin Mai Na Ƙasashen Larabawa Da Su Bar Wuraren Cikin Gaggawa 

Iran Ta Gargaɗi Jama'ar Da Ke Kusa Da Cibiyoyin Matatar Mai Na Ƙasashen Larabawa Da Su Bar Wuraren Cikin Gaggawa + hatuna

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kakakin Cibiyar Hazrat Khatamul Anbiya (SA): Maƙiyi masu aikata laifuka ta hanyar kai hare-hare kan wani ɓangare na albarkatun mai da makamashi na Iran a kudancin ƙasar. Kamar yadda muka yi gargadi a baya, idan aka kai hari kan cibiyoyin man fetur, makamashi da iskar gas da tattalin arzikin kasarmu, za mu kai hari kan ƙasar da ta kawo harin ta'addanci da kai hari kuma cibiyoyinsu sun zamo hadafin hari halastacce garemu. Kai hari kan cibiyoyin samar da man fetur, makamashi da iskar gas na kasar da ta kawo mana hari sun zama halastattun hadafin wajen mayar da martani mai karfi da tsanani.

Makiya su jira matakin da sojojin Jamhuriyar Musulunci suka dauka. 

Wuraren da aka bayar da umarnin nisantarsu a ƙasashen Saudi Arabia, UAE da Qatar. Sun haɗa da: waɗannan wurare 

1) Samarf Refinery - Saudi Arabia 

2) Cibiyar Gas ta Al-Hisni- Hadaddiyar Daular Larabawa 

3) Al-Jubeil Petrochemical Complex - Saudi Arabia 

4) Musaid Petrochemical Complex da Kamfanin Musaid Kamfanin Chevron) - Qatar 

5) matatar Ra'as Lefan (yankuna na 1 da 2) - Qatar Waɗannan cibiyoyin sun zama halastattun hadafi kai tsaye kuma na halal kuma za a a kai hari kansu cikin sa'o'i masu zuwa. 

Don haka, ana kira ga dukkan 'yan ƙasa, mazauna da ma'aikata da su bar waɗannan wuraren nan da nan kuma a kai su zuwa tazara mai aminci ba tare da wani bata lokaci ba. 

A baya can, an yi wa sarakunan ku gargaɗi na gaskiya da kuma maimaita gargaɗi game da shiga wannan hanya mai haɗari da zamba ga makomar al'ummominsu.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha