31 Janairu 2026 - 19:56
Source: ABNA24
Iran A Shirye Take Ta Mayar Da Martani Fiye Da Yadda Ake Tsammani

Tehran ta yi gargadin cewa duk wani matakin soja da za a ɗauka kan Iran, ba tare da la'akari da iyakokinta ba, za a gamu da martani mai faɗi; matsayin da ke nuna ƙoƙarin ɓangarorin na yin tasiri ga lissafin juna a lokacin yanke quduri mai mahimmanci.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A tsakanin nan alamun ƙaruwar shirye-shiryen sojojin Amurka a yankin yana karuwa, hasashe game da yiwuwar faɗan soja da Iran ya sake zama abin da masu sharhi ke mayar da hankali a kai. A lokaci guda, Tehran ta sanar da shirye-shiryenta na mayar da martani ga duk wani matakin soja inda ake ta magana game da yiwuwar yin atisayen haɗin gwiwa da Rasha da China a cikin ruwan yankin; ci gaban da zai iya shafar lissafin Washington.

A cewar wani rahoto da gidan yanar gizon Noshre ya buga, ana ɗaukar sa'o'i masu zuwa a matsayin masu mahimmanci don tantance alkiblar ci gaban tsaro a yankin. Majiyar ta yi iƙirarin cewa batun atisayen haɗin gwiwa tsakanin Iran, Rasha da China a cikin Tekun Oman da Tekun Indiya na iya shafar yanayin yanke qudurin sojojin Amurka kuma yana jefa shakku kan yanayin gaggawa da ba’a zata da tsammanai ba.

A cewar rahoton, shirye-shiryen sojin Amurka sun yi daidai da yadda ake yunkurin nufatar kayayyakin more rayuwa na Iran a cikin da'irori na nazari, kodayake jami'an Washington ba su ɗauki wani matsayi a fili ba kan wannan batu. Akasin haka, Iran ta ƙara matakin shirye-shiryenta na soja, tana dogaro da haɗin gwiwar tsaro da Moscow da Beijing.

Majiya ta ƙara da cewa a cikin kimantawar da aka yi, Rundunar Sojan Ruwa ta Iran tana ɗaya daga cikin manyan manufofin kowane irin hari da AMurka zata kai; wani mataki da za a iya aiwatarwa da nufin takaita damar Iran ga ruwa mai faɗi da kuma shafar fitar da mai. Wannan batu yana da matuƙar muhimmanci, musamman daga mahangar China, a matsayin ɗaya daga cikin manyan wuraren da ake fitar da mai na Iran, kuma yana bayyana dalilin Beijing na taka rawa sosai a cikin siyasar daidaiton yankin.

Ko da yake har yanzu ba a fayyace irin ƙarfin da masu ruwa da tsaki na Gabas za su iya yi ba, da alama waɗannan ƙungiyoyin za su ƙara farashin duk wani matakin soja da kuma ci gaba da buɗe sararin diflomasiyya har zuwa mataki na ƙarshe.

A halin yanzu, wasu masu sharhi suna ganin cewa Shugaban Amurka Donald Trump, idan ya ja da baya, zai buƙaci gabatar da wani gagarumin nasara a fagen cikin gida. Saboda haka, ana tada yiwuwar Washington ta bi wani yanayi na ɗan gajeren lokaci; yanayin da ke da nufin matsa lamba sosai da kuma tilasta wa Tehran ta amince da sharuɗɗan siyasa.

A akasin haka, Tehran, bayan ta fahimci irin wannan yiwuwar, ta yi gargaɗin cewa duk wani matakin soja da za ta ɗauka kan Iran, ba tare da la'akari da girmanta da fadadarsa ba, za ta mayar da martani mai faɗi gwagwargwadon yadda akai ma ta; matsayin da ke nuna ƙoƙarin da ɓangarorin ke yi na yin tasiri ga lissafin juna a wannan yanayi na yanke yunkuri da qudiri mai mahimmanci.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha