Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): A cikin duniyar da ke cike da rudani a yau, inda damuwa ta zamo baƙon da ba a gayyace ta ba a cikin zukata, rayuwar Annabin Rahama (SAW) tana gabatar mana da taswirar samun aminci. Ya gina mana mafaka mai aminci daga guguwar kuncin ruhi ta hanyar addu'a da anbaton Allah.
Ambaton Allah; Abu Mai Tasiri A Samar Nutsuwa Da Alqur'ani Ya Tabbatar
Annabi (SAW) yana dogara da ambaton Allah a cikin mawuyacin lokacinsa na damuwa. Alqur'ani Mai Tsarki ya tabbatar da wannan ka'ida da kyau:
«الَّذِینَ آمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِکْرِ اللَّهِ ۗ أَلَا بِذِکْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ»[۱]
"Waɗanda suka yi imani kuma zukatansu suke samin natsuwa cikin ambaton Allah. Tabbas da ambaton Allah ne zukata ke samun natsuwa."[1]
Ya jaddada a maganarsa wajen yin zikirai kamar:
«لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّهَ إِلَّا بِاللَّهِ»[۲]
"Babu Tsimi Babu ƙarfi sai ga Allah"[2]
Wannan addu’ar tana warkar da damuwar da ke fitowa daga jin gazawa da rashin samun taimako kuma tana maye gurbinta da ikon Allah mara iyaka.
Addu'a; Ganawa Mai Waraka A Mafi Kyawun Nau'ika
A rayuwar Manzon Allah (SAW), addu'a ba wai kawai ibada ba ce, Sai dai ta zamo kayan aiki ne mai tasiri don sarrafa damuwa ta yau da kullun. Ya ce: «الدُّعَاءُ سِلَاحُ الْمُؤْمِنِ»[۳]
"Addu'a makamin mumini ce."[3] Daga cikin addu'o'insa na neman sauƙi daga nauyin damuwa mai nauyi akwai:
«اللَّهُمَّ إِنِّی أَعُوذُ بِکَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحَزَنِ...»[۴]
"Ya Allah, ina neman tsarinka daga damuwa da baƙin ciki..."[4] Waɗannan addu'o'in zuciya suna sanya nauyin tunanin mutum a kan kafadun alheri, wanda ke iya magance kowace matsala.
Wanda Ya Rubuta: Hujjatul-Islam wal-Muslimeen Muhammad Hussain Amin/ Marubuci kuma malamin addini
Wanda Ya Fassara: SK
[1] Suratul Ra’ad, aya ta 28
[2] Al-Kafi, juzu’i na 2, shafi na 553
[3] Bihar al-Anwar, juzu'i na 93, shafi na 295
[4] Sahihul Bukhari, juzu'i na 7, Kitab al-Dawaat, hadisi na 3
Your Comment