Jagora ya fara da taya murnar Mauludin Imam Hussain (AS) wanda ya kasance a ranar 3 ga Sha'aban, da na ƙaninsa Sayyid Abul Fadl Abbas (AS) da ya auku a ranar 4 ga Sha'aban, da kuma na ɗansa kuma magajinsa Imam Zainul Abidin (AS), wanda aka haifa ranar 5 ga watan Sha'aban.
Yace, haihuwarsu a shekaru ne daban-daban, amma duk ya fado ne a watan Sha'aban. "Sha'aban dama wata ne na haihuwar Sahibul Asr waz Zaman (AS), wanda ya zo a tsakiyar watan, sai ya zama kuma haihuwar kakanninsa Imam Husaini da Imam Zainul Abidin, da kuma na Babbansa Abul Fadl Abbas (AS).”
Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi bitan darajoji daban-daban na kowanne daga gwarazan na Karbala, inda ya bayyana Imam Husaini (AS) a matsayin abin koyi, wanda ya sadaukar da kansa saboda addini. Yace, “Tsayuwar (Imam Husaini) ya nuna mana mafita shi ne tsayawa kyam a tafarkin Allah. Su wadanda suka kashe shi, sun dauka sun gama da addini kenan, ashe ba su sani ba, sun raya addinin ne ta yadda basu tsammani.”
Da yake bayani dangane da Sayyid Abul Fadl Abbas, Jagora ya bayyana cewa, shi duk rayuwarsa yana taimakon Imam Husaini (AS) ne. Inda ya kawo kissar yadda Imam Husaini ya ma babansa Amirulmumin (AS) albishir a lokacin da aka haifi Abul Fadl, wanda a karshe Amirulmumin ya shaida ma Imam Husaini cewa, shi ne mataimakinsa. A nan Jagora ya bayyana yadda Abul Fadl ya taimaki Imam Husaini (AS) har ƙarshen numfashinsa.
Haka kuma Jagora ya bayyana Imam Zainul Abidin a matsayin gwarzon Karbala, wanda duk abinda ya faru akan idonsa ya faru. Yace: "Duk abinda ya faru a Karbala akan idonsa aka yi, kuma aka saka masa sarka aka tafi da shi.”
A karshe, Jagora ya yi tuni akan jarabawa da al'adarta. Yace: “In goguwar bala'i ta zo (jarabawa kenan), wasu su dake, wasu kuka su kasa dakewa. To, jarabawa aka ma wadannan bayin, duk suka dake, suka zama mana abin koyi.”
Yace: “Musamman muke cewa, shi Abul Fadl Abbas ba kawai abin koyi ne ga matasa ba, abin koyi ne ga dukkanin al'umma, amma musamman matasa. In ana tuna shi, da gwarzontaka irin ta shi, ya kamata ya zama ramzi ne ga matashi, ta yadda zai ba da ransa ya tsaya ƙyam, ba ko gezau, har izuwa cikawa.”
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Your Comment