Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: kafofin watsa labaran Isra'ila, sun ambato wani rahoto na Iran, suna masu bayyana cewa hukumomin tsaron Iran sun canza hanyar sadarwa ta tauraron dan adam ta Elon Mask ta Starlink zuwa abin da suka bayyana a matsayin "tsarin leken asiri a gwamnatance" da suke amfani da shi ga masu tarzoma da masu tayar da zaune tsaye a lokacin rikicin.
Rahoton ya nuna cewa abin da ake ɗaukarsa a matsayin "layin ceto" ga masu tarzoma, wanda ke ba su damar haɗuwa da duniyar waje, ya zama kayan aiki mai tasiri a kansu. Bayanan sun nuna cewa hukumomin Iran ba su kasa toshe Starlink da farko ba, sai dai suna sane suka bar hanyar sadarwa a bude a matsayin "tarkon zuma".
Rahotan sun kara da cewa da zarar masu tarzoma sun yi amfani da hanyar sadarwa don watsa abubuwan da ke faruwa a ƙasashen waje, Rundunar Juyin Juya Hali ta gudanar da ayyukan bin diddigin wuri daidai da nufin masu amfani da na’ura ɗin, wanda ya kai ga kama su kafin a rufe na’ura ɗin har abada.
Rahoton yayi ishara da cewa, a cewar wannan labarin, gwamnatin Iran ta yi nasarar lalata fuskar "fasahar Yammacin duniya da ba za a iya cin galaba a kanta ba," tana mai aika sakon gargadi mai ban tsoro ga masu kawo tarzoma: "Babu wajen ɓuya," wanda ya ke har tauraron dan adam ta Amurka "suna aiki ne don goyon bayan gwamnatin Iran".
A cewar kafofin watsa labarai na Isra'ila, wannan tsari yana nuna yadda Iran ke da ci gaba a fannin yaƙi ta yanar gizo da ta lantarki, wanda wataƙila "wanda ƙwarewar Rasha ko China ke tallafawa," musamman wajen gano hanyoyin sadarwa daga tashoshin tauraron dan adam.
Rahoton ya nuna cewa zurfin tasirin ba wai kawai ya takaita ga kama mutane daga wurare ba ne, har ma yana nufin haifar da rashin yarda da amincewa ga sadarawar ga masu tarzoma da masu daukar nauyinsu, don haka duk wata hanyar kauce wa rufewar ana ɗaukarta a matsayin wata dabara da gwamnatin za ta iya yi, idan aka yi la'akari da cewa Iran "ba wai kawai ta kashe fitilun ba ne, har ma ta sa abokan gaba ji tsoron kunna ashana".
Your Comment