23 Janairu 2026 - 15:20
Source: ABNA24
Murna Da Haihuwar Imam Husain As Ga Daukacin Al’umma Duniyawa

A irin wannan rana ne 3/shaaban/4h wanda ya dace da ranar Alhamis aka haifi Sayyidush shuhada’a Imam Husain As a birnin madina shekarata 4h.

Imam Husain As dai kamar yadda muka sani Da ne ga Sayyidah Fatimah da Imam Ali As jika ga manzon Rahama sawa kane g Imam Hasan As kuma shida Yayansa Imam Hasan sune shugabanni Samarin gidan Ajannah.

Bayan haihuwarsa Manzan Allah ya gudanar masa da dukkan abubuwan da ake yiwa jariri bayan haihuwarsa na kiran Sallah da sa masa suna bayan kwana bakwai yayi umarni da ayi masa yankan suna da Rago aka raba naman ga mutane kuma yayi umarni da aske masa gashin kansa dayin sadaka gwargwadon gashin sa.

Yazo a Littafan tarihi Lokacin da aka gayawa Annabi Busharar Haihuwarsa ya tashi da sauri yaje Gidan Diyarsa Sayyidah fadimah As bayan shigarsa ya rinka tafiya a sannu damuwa ta bayyana a fuskarsa ya kira Asma’au kan ta kawo masa Dansa.

Bayan ta kawo shi ya rungume shi yayi ta subtarsa sannan ya fashe da kuka sai Asma’au ta rude da wannan yanayi da taga Annabi a ciki tace masa: fansarka babana da babata me yasa kake kuka?

Sai ya Amsa mata da cewa: Ina yin kuka ne saboda abinda zai same dana ne’ sai tace yanzu fah aka haife shi sai yace mata cikin sassaukar murya yace: Gungun Azzalumai zasu kashe shi a bayana kar Allah yabani cetansu. Sannan ya radama Asmau da cewa: kar tagayawa Sayyidah fadimah As saboda tana cikin murnar haihuwarsa.

Imam Yarayu tsawon shekaru 57 ya dauki shekaru 11 yana jagorantar Al’umma.

Your Comment

You are replying to: .
captcha