Sakon shugaban ƙasar Iran ga al'ummar Iran game da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan
Shugaban ƙasar Iran: Makircin Amurka Da Sahayoniyawa a watan Janairu 2026 ramuwar gayya ce ta matsorata makiya al'ummar Iran daga shan kaye a yakin kwanaki 12.
Al'umma Iran Madaukakiya abubuwan da suka faru a satukan da suka gabata garemu wata jarabawa ce mai tsanani da wahala wacce ta bar tasirin radadi tsanani.
Waɗannan abubuwan masu ɗaci da ban tausayi sun kasance mafi zafi da rashin yarda agareni a matsayina na shugaban ku da kuka zaɓa. Makircin da maƙiya Iran suka yi na canja fagen zanga-zanga lumana ta al'umma zuwa fagen yaki da zubar da jini da tashin hankali wanda ya yi sanadin mutuwar 'yan kasa kusan dubu 3,000 na wannan kasa da kuma aukar da raunuka na jiki da na ruhi na dubban wasu.
Su ne dai mugayen hannayen da a cikin yakin kwanaki 12 suka jika hannayensu da jinin mata, maza, matasa, yara, masana kimiyya da kwamandojin wannan yanki, sun fito ta ɗayana hannun rigarsu a yau, kuma ta hanyar wasu sojojin haya sun canja zanga-zangar lumana wacce al'umma sukai bisa haƙƙin dabi'a da al'umma masu kuzari da fara'a, sun mai da ta zama ta fusata da rashin tsarki, wanda a cikinsa aka mayar da daruruwan masallatai da makarantu, wuraren jama'a da kadarorin kasa zuwa toka.
An rasa rayuka masu daraja kuma an cuɗanya jikkunan ababen ƙauna cikin jini. Shahadar kusan mutane 2,500 da ba su ji ba ba su gani ba da jami'an tsaro a cikin 'yan kwanaki na hargitsi da rashin aminci wani lamari ne mai guba da aukuwarsa yana da matukar wahala ga Iran dinmu kamar sauran manyan abubuwan da suka faru.
Makircin Amurka Da Sahayoniyawa a watan Janairu 2026 ramuwar gayya ce ta matsorata makiya al'ummar Iran daga shan kaye a yakin kwanaki 12.
A yau, ina cikin baƙin ciki ga dukan rayukan da mu kai rashinsu da kuma juyayi ga dukkan ƴan ƙasa ta waɗanda suka shiga baƙin ciki mai girma a kwanakin nan, kuma bisa matsayi da alhakin da ya samo asali daga amanar da babbar al'ummar Iran ta bani, ina tunatar da ku tabbatuwa ta game da alkawarin da na ɗauka na kare hakkin a al'umma.
Na umurci cibiyoyi daban-daban da su binciko da gano dalilan faruwar wadannan lamurra tare da kawar da shafe tushen waɗannan masu tayar da hankali da suka sabbaba abubuwan da suka faru. Zanga-zangar lumana hakki ne na 'yan kasa kuma wajibi ne gwamnati ta ji muryar jama'a.
A cikin binciken lamarin da kuma wadanda tuhuma ake tsare da su na baya-bayan nan, za a ba da kulawa sosai don tantance sahun masu zanga-zangar har ma da wadannan aka yaudarar daga wadanda suka dulmiya hannayensu da jinin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ta hanyar yin adalic.
Gwamnati da mahukuntan ta suna da alhakin duk wadanda abin ya shafa a cikin wadannan munanan al'amura, kuma tare da taimako al'ummar mai shirya ta Iran, za ta kokarin da zata iya yi wajen rama da biyan diyya gwargwadon iko.
Gano wuraren da ake da rauni da kuma gyara su da daukar darasi daga abubuwan da suka faru masu ɗaci zai share fagen gaba, kuma babbar al'ummar Iran za ta tsara makoma mai haske da kwanciyar hankali a inuwar hadin kai da hadin gwiwa da kuma tausayawa dakaru uku da ke karkashin jagorancin shugaban koli. Insha Allah
Your Comment