21 Janairu 2026 - 21:39
Source: ABNA24
Kremlin: Mahmoud Abbas Da Witkoff Za Su Gana Da Putin Ranar Alhamis

Kremlin ta sanar da cewa: Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da wakilin musamman na shugaban Amurka Donald Trump Steve Witkoff za su gana a kebe da shugaban Rasha Vladimir Putin a ranar Alhamis.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Witkoff ya kuma sanar da tafiyarsa zuwa Rasha tare da mai ba shugaban Amurka Trump shawara kuma surukinsa Jared Kushner, yana mai cewa:

Za mu isa Moscow a daren yau, sannan mu je Hadaddiyar Daular Larabawa don halartar tarurruka kan shirin zaman lafiya.

Your Comment

You are replying to: .
captcha