21 Janairu 2026 - 19:26
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Kashe 'Yan Jaridar Falasdinawa 3

Majiyoyin Falasdinawa sun ruwaito cewa sojojin Isra'ila sun kai hari kai tsaye kan wata mota kirar Jeep da ke dauke da gungun 'yan jarida kusa da Asibitin Turki da ke tsakiyar Zirin Gaza.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Harin ya yi sanadiyyar shahadar 'yan jarida uku da kuma raunata wasu da dama, wadanda aka ruwaito cewa wasu daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.

A cewar wadannan rahotanni, 'yan jaridar da aka kai hari suna gudanar da wani aikin jarida tare da daukar hoton wani sansani da ke da alaƙa da "Kwamitin Masar" a yankin; Kwamitin Masar Wata kungiya ce da ta dade tana aiki a cikin 'yan watannin nan a fannin samar da agaji da kuma samarwar da 'yan gudun hijirar yaki a Gaza wuraren fakewa.

Shaidu sun jaddada cewa motar da aka kai hari ta kasance ta fararen hula da kafofin watsa labarai kuma ba a ga wani aikin soja a wurin ba.

Isra'ila Ta Kashe 'Yan Jaridar Falasdinawa 3

A cewar shaidar gani da ido, an kai gawarwakin shahidai da wadanda suka jikkata zuwa cibiyoyin lafiya kuma kungiyoyin agaji suna fuskantar karancin kayan aikin likitanci.

Your Comment

You are replying to: .
captcha