Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Gobarar ta auku a yankunan dajin mafi girma wanda ya kasance a yankunan Noble da Biobio, ya zuwa yanzu ya tilasta wa mutane 20,000 tserewa daga gidajensu.
Gwamnatin Chile ta ayyana dokar ta baci a wadannan yankuna biyu. Rahotanni sun ce gobarar ta kone dajin da ya kai kimanin hekta 8,500 kuma ta lalata gidaje akalla 250.
Your Comment