17 Janairu 2026 - 11:48
Source: ABNA24
Murna Da Ranar Mab’ath: Bamu Aiko Ka Ba Sai Domin Ka Zama Rahama Ga Talikai

27 Rajab 13 Kafin Hijrah Ranar Da Allah Ta’ala Ya Aiko Manzon Rahama {Sawa} Ga Dukkan Halittun Duniya

            A irin wannan rana ne Allah ta’ala yaiwa Al’ummar duniya gaba ki daya tagomashi na Aiko masu da Annabin Rahama cika makon Annabawa Shugaban Manzanni Annabi Muhammad Sawa hakan ya faru a lokacin da Monzon Rahama ya kai shekaru 40 na Rayuwarsa Mala’ika Jibrail As yazo masa da sakon Ubangiji na Busharar kasancewarsa Annabi Manzon na wannan Al’umma lokacin yana Kogon Hira in da ya karanta masa farkon Ayoyi Biyar na Surar Alak:

بسم الله الرحمن الرحيم

اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ (1) خَلَقَ الْإِنْسَانَ مِنْ عَلَقٍ (2) اقْرَأْ وَرَبُّكَ الْأَكْرَمُ (3) الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ (4) عَلَّمَ الْإِنْسَانَ مَا لَمْ يَعْلَمْ (5)

  bayan ya saurare wanann bushara ya koma zuwa gida yana me dauke da nauyin wannan sako ya kwanta akan shinfidarsa sai Mala’ika ya sake sauka da wahayi na Biyu na Ayoyi uku na surar Mudassir:

بسم الله الرحمن الرحيم

يَاأَيُّهَا الْمُدَّثِّرُ (1) قُمْ فَأَنْذِرْ (2) وَرَبَّكَ فَكَبِّرْ (3)

 sai Annabi ya tashi ya fara Aikin kira zuwa ga Allah wanda ya fara kira kuwa ta kasance matarsa Sayyidah Khadijah As Da dan Baffansa Imam Ali As. Sannan bawansa Zaidu dan Harisa Rd wadannan sune suka fara Imani da Annabin a matakin farko na wannan Kira.

Bayan haka Annabi yakan sanar da Abokansa na kusa da shi a tsakanin kawukansu bai kira mutane gaba daya ba har bayan shekaru da aiko shi kana wani sakon yazo yana mai cewa:

{ وَأَنْذِرْ عَشِيرَتَكَ الْأَقْرَبِينَ (214) وَاخْفِضْ جَنَاحَكَ لِمَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ (215) فَإِنْ عَصَوْكَ فَقُلْ إِنِّي بَرِيءٌ مِمَّا تَعْمَلُونَ (216) }

a lokacin ne kiransa a Bayyane ya fara.

Ibn Is’hak dangane da hakan ya kawo a littafin tarihi da ya rubuta cewa: yayin da wadannan ayaoyin su ka sauka sai Annabin Sawa y ace Ali as ya Ali as Ubangiji ya umarce ni da in kirawo dangi na kusa don su bauta masa; Ku yanka wata tunkiya, ku shirya sa'i kofi guda na burodi, sai Ali (a.s) ya yi haka, sai a wannan rana mutane kusan arba'in ko kusan arba'in daga cikin 'ya'yan Abdul Muddalib suka zo suka ci suka sha har suka koshi da abinci. Manzon Allah ya so ya fara magana sai Abu Lahab ya ce “shi ya sihirce ku”.

Taron anan ya watse. Sai Manzon Allah ya sake kiransu a wata ranar ya ce: “Ya ku ‘ya’yan Abdulmuddalib, ba na zaton wani Balarabe ya zo da wani abu mafi alheri ga mutanensa sama da abin da na zo muku da shi. Na zo muku da duniya da lahira, Yunus bn Bukir, wanda daya ne daga cikin maruwaitan Ibn Ishaq, ya rubuta maganar Manzon Allah (saww) har zuwa wannan gabar, kuma (ban sani ba da gangan ko mantuwa) bai kawo sauran ba. Ibn Hisham, wanda ya ruwaito daga Ibn Ishaq ta hanyar Shekh Baka’i, ya kawo ayar ne kawai bai kara mata komai ba.

Amma Tabari, wanda daya ne daga cikin tsoffin masana tarihi kuma littafinsa yana cikin rubuce-rubucen farko, ya rubuta cewa:

Yayin da Manzon Allah (saww) ya aika da gayyatarsa ​​zuwa ga ‘yan uwansa, sai ya ce: Waye a cikinku zai taimake ni a cikin wannan al’amari ya zamo dan’uwana da magajina da halifana a cikinku? Sai kowa ya yi shiru, sai Ali (a.s.) ya ce: “Ya Manzon Allah, ni ne. Annabi ya ce: "Wannan ne magajina kuma halifana a cikinku". Ku saurare shi kuma ku yi masa biyayya.

Haka nan kuma wasu masana tarihi da marubuta Seerah sun ruwaito wannan ruwaya, kuma tana daga cikin shahararrun hadisai. Misalin irin wannan da sauran su ma Tabari ya rubuta daga Ibn Abbas cewa wata rana Manzon Allah ya je Dutsen Safa ya kira Kuraishawa zuwa gare shi, sai ya ce musu: “Idan na ba ku labarin cewa abokan gaba za su zo muku da safiya ko da yamma, shin, zã ku yarda da ni?" Sai suka ce: "Na'am".

Hadafin Aiko Annabin Rahama Muhammad (S):

Allah Ta’ala Ya Ce: ( Ya kai wannan annabi mun aiko ka ne omin ka zama mai shaida da yin bushara da yin gargadi) kuma mai yin kira zuwa ga Allah da izininsa kuma zamo fitla mai haskakawa) kuma kayiwa muminai bushara da samun falala mai girma daga wajen Allah) kuma kada kayiwa kafirai da munafukai biyayya ka kyale dukkan cutarwarsu gareka ka kuma dogara ga Allah domin ya ishe ya zama mai kulawa da kai).

يَاأَيُّهَا النَّبِيُّ إِنَّا أَرْسَلْنَاكَ شَاهِدًا وَمُبَشِّرًا وَنَذِيرًا (45) وَدَاعِيًا إِلَى اللَّهِ بِإِذْنِهِ وَسِرَاجًا مُنِيرًا (46) وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ بِأَنَّ لَهُمْ مِنَ اللَّهِ فَضْلًا كَبِيرًا (47) وَلَا تُطِعِ الْكَافِرِينَ وَالْمُنَافِقِينَ وَدَعْ أَذَاهُمْ وَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ وَكَفَى بِاللَّهِ وَكِيلًا (48)

Ibn Hisham ya rubuta cewa: “Da farko Manzon Allah (SAW) ya kira Kuraishawa zuwa ga bautar Ubangiji daya, amma ba su kai masa hari ba. Amma kiyayyarsu gareshi ta fara ne yayin da ya fara tozarta gumakansu ayoyin kur’ani ma sun yi nunu da hakan:

} وَإِذَا رَآكَ الَّذِينَ كَفَرُوا إِنْ يَتَّخِذُونَكَ إِلَّا هُزُوًا أَهَذَا الَّذِي يَذْكُرُ آلِهَتَكُمْ وَهُمْ بِذِكْرِ الرَّحْمَنِ هُمْ كَافِرُونَ (36)

Your Comment

You are replying to: .
captcha