29 Satumba 2025 - 08:50
Source: ABNA24
Iran: An Rataye "Bahman Choubi-Asl", Amintaccen Ɗan Leƙen Asirin Isra’ila

An zartar da hukuncin kisa kan Bahman Choubi-Asl daya daga cikin manyan jami'an leken asirin gwamnatin sahyoniyawa a Iran bayan bin matakan shari'a tare da tabbatar da hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: an zartar da hukuncin kisa kan Bahman Choubi-Asl daya daga cikin manyan jami'an leken asiri na gwamnatin sahyoniyawa a kasar Iran bayan bin matakan shari'a tare da tabbatar da hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke.

An rataye Bahman Choubi-Asl Hassan wanda ke da cikakken hadakayyar aiki tare da jami'an leken asiri Isra’ila a fagen tattara bayanai a safiyar yau bayan ya bi hanyar da doka ta tanada.

Bahman Choubi-Asl kwararre ne kan harkokin bayanan database wanda ya shiga aikin kula da harkokin sadarwa na kasar ta hanyar kasancewarsa a wani kamfanin kimiyya.

Saboda kwarewarsa, Choubi-Asl ya kasance a matsayin manaja a duk ayyukan kamfanin kuma yana da damar samun mahimman bayanai na kasar.

Yadda Ya Kulla Alaka Da Hukumar Leken Asiri

Bayan samun digirin sa na ƙwarewa a fannin bayanai, Bahman Choubi jami'an Mossad ne suka nuna shi a lokacin da yake halartar kwas na ƙwararru a ɗaya daga cikin ƙasashen Takun Farisa.

Bayan wani lokaci, wani jami'in Mossad ya tuntubi Choubi a karkashin sunan wani kamfani mai suna ESMI kuma ya gayyace shi don ba da hadin kai a ayyukan adana bayanai yayin wata hira ta wayar tarho.

Bayan haka, bisa zargin gudanar da tattauanwa na kwararru da kuma yin magana a kai tsaye game da sharudan hadin gwiwa, aka bukaci wanda ake kara ya tafi kasar Armeniya, amma bayan wani lokaci, sai aka canza inda za a yi tafiya zuwa Indiya, aka umarce shi da ya zo da kwamfutar tafi-da-gidanka. A cewar wanda ake zargin, ya dauki kwamfutar tafi da gidanka ne a tafiyarsa zuwa kasar Indiya, wanda ya saba yin aikin.

A lokacin tafiya da aka ambata, manajan kamfanin ESMI, yayin da yake ba da labari ga wanda ake tuhuma, samun dama da kuma kimanta kwarewar fasaha, ya biya duk kudaden tafiya kuma ya ba shi kyauta, kuma don inganta kwarewarsa na sirri da na sana'a, an bashi dama don halartar azuzuwan horon fasaha.

Dangane da haka, manajan kamfanin ESMI (wani jami'in Mossad) ya gayyaci Bahman Choubi-Asl zuwa Ireland, kuma wanda ake tuhuma ya halarci kwasa-kwasan horaswa na musamman a wannan ƙasa na kusan kwanaki 45. A wannan lokaci, an gabatar da wani sabon mutum da ya kware a harshen Farisa ga Bahman Choubi-Asl, kuma ta hanyar biya masa kudin kos din da kuma kudin masauki, bayan tarurrukan bayanan sirri da dama, Bahman Choubi-Asl ya yi bayani dalla-dalla tare da tantance shi a fagen kwarewarsa da ayyuka masu muhimmanci da ake aiwatarwa, da kuma batun tsarin tattara bayanai da ayyukan cibiyoyin tattara bayanai na Iran.

Bukatun Da Mossad Su Ke So

A cikin bayanansa, wanda ake tuhuma ya yi ishara da wasu bukatu na makiya a wadannan fagage.

Domin ya samar da damar kutsawa cikin tsarin cibiyar bayanai na cibiyoyi daban-daban, kutsawa tare da samun bayanai na kamfanoni na musamman masu aiki a fagen kayan lantarki da bayanan sirri, kutsawa tare da ayyuka masu mahimmanci ga ababen more rayuwa, kulla alaka da kutsawa tare da fitattun mutane da masu iya aiki a fagen bayanan Oracle, da ayyukan da ma’aikatan Mossad ya ba su. Babban manufar hukumar ta Mossad ita ce ta jawo hankalin wanda ake tuhuma, da samun bayanan hukumomin gwamnati, da kuma haifar da sabani a cibiyoyin tattara bayanai na Iran, wanda kuma ya ci gaba da bin wasu manufofi na biyu, ciki har da binciken hanyar shigo da kayan lantarki daga waje...

Yin Aikin Leken Asirin Wanda Aka Yankewa Hukuncin Kisan Da Gangan

Ganin irin ayyuka da goyon bayan wanda aka yankewa hukuncin na karfin harshe da kuma inganta kwarewa na musamman don samun aikin, gudanar da tarurruka 63 a balaguro 9 na kasashen waje da kuma tarurruka 95 da ba a fuska da fuska tare da jami’an Mossad da karbar kayan aikin leken asiri, amintattun na’urorin sadarwa da kuma karbar wasu kudade na musamman, ya nuna cewa mai laifin ya ba da hadin kai sosai tare da hukumar leken asiri ta Mossad.

Kasashen UAE, Armenia, India, Thailand, Vietnam, Ireland da Bulgaria na daga cikin kasashen da Bahman Choubi ya gana da jami'an Mossad da kan sa.

Bayan kama wanda ake tuhuma tare da kammala bincike, an bayar da sammacin kama shi da kuma tuhume-tuhume kan laifukan leken asiri da ake yi wa jamhuriyar Musulunci ta Iran, tare da bayyana yadda aka samu kudade da hadin gwiwar leken asiri tare da hidimtawarsa ga gwamnatin yahudawan sahyoniya, da kuma aika shi zuwa kotu.

A karshe bayan kammala zaman kotun a gaban lauyan wanda ake tuhuma tare da bin ka'idojin shari'a da kuma duba takardun, an yankewa Bahman Choubi hukuncin kisa kan zargin fasadi a doron kasa ta hanyar hadin gwiwar leken asiri da hidimtawa gwamnatin Sahayoniyawan.

Bayan daukaka kara, an aika karar zuwa Kotun Koli, wacce bayan ta duba karar ta yi watsi da karar tare da tabbatar da yanke hukuncin.

An zartar da hukuncin ne bayan kotun koli ta tabbatar da shi a safiyar yau.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha