4 Agusta 2025 - 23:20
Source: ABNA24
Me Yasa Sojojin Yahudawan Sahyoniya Suke Tunanin Kashe Kansu?

Duk da take-taken karya da sojojin yahudawan sahyoniya da majalisar ministocin kasar suka yi na "babbar nasara" a yakin Gaza da kuma ikirarin da suke yi na ruguza ikon Hamas, yawan kashe-kashen kai da sojojin Isra'ila ke yi na nuni da wata hakika da ke nuni da babban rikicin gwamnatin kasar a yakin.

Kamfanin dillancin labaran Ahlulbayt na kasa da kasa (ABNA) ya habarta cewa: Wani rahoton bincike ya nuna cewa: Duk da cewa asalin tushen kashe kawuna a cikin sojojin Isra'ila shi ne yakin da gwamnatin kasar ke yi da kasar Labanon; musamman yakin Yuli na 2006 da kuma guguwar kisan kai a tsakanin sojojin yahudawan sahyoniya masu fama da tabin hankali daban-daban, ciki har da "cutar damuwa bayan yakin." 

Wannan al'amari ya bayyana a fili bayan harin Dufanul Aqsa, da sojojin gwagwarmayar Palasdinawa suka gudanar a ranar 7 ga Oktoba, 2023. Tun daga farkon yakin Gaza, kuma duk da cewa sojojin yahudawan sahyoniya sun kafa wata manufar yin katsalandan na soji a kafafen yada labaran gwamnatin kuma hana buga sahihin alkaluma kan wadanda suka mutu, a fagen daga da kuma ta hanyar kashe-kashen kai, a cewar majiyoyin Ibraniyawa sun yi gargadin cewa sojojin Isra'ila suna dada samun hauhawa da karuwar yin kasan-kai.

Wani yanayin na yin kisan kai na baya-bayan nan da sojojin Isra'ila suka yi ya watsu a kafafen yada labarai shi ne na Ariel Taman, wani sojan ajiya a cikin sojojin mamaya, wanda ya kashe kansa a gidansa da ke kudancin Falasdinu da suka mamaye. Sojan yahudawan sahyoniya ya yi aiki a sashin tantance jikin sojojin Isra'ila, daya daga cikin ayyuka masu wuyar sha’ani ta fuskar rikita tunani. Tashar talabijin ta Channel 12 ta Sahayoniyya ta bayar da rahoton cewa, a tsakiyar watan Yuli kadai wasu sojojin Isra'ila hudu suka yi yunkurin kashe kansu, kuma adadin wadanda suka kashe kansu a cikin sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila ya karu matuka idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata tun bayan fara yakin.

Me Yasa Sojojin Yahudawan Sahyoniya Suke Tunanin Kashe Kansu?

A tsawon lokuta daban-daban na yakin da babu iyaka da wannan gwamnati ta yi da kasashen larabawa, musamman al'ummar Palastinu, sojojin gwamnatin sahyoniyawan sun aikata laifukan da ba za su iya misaltuwa ba, kuma ba za su iya yin tunanin aikata hkan ba ga wani dan Adam ta fuskar zalunci da dabbanci. A dabi'ance, ko da ganin kadan daga cikin wadannan laifuffuka yana haifar da mummunar illa ta tunani ga daidaikun mutane; amma sojojin yahudawan sahyoniya ba jin komai da aikata hakan ko yin nadama bayan aikata wadannan laifuka, sai dai ma suna alfahari da wannan dabbanci da yada hotunanta a kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta.

Tun farkon yakin Gaza, kafafen yada labaran gwamnatin sun buga rahotanni da dama game da tabin hankali da raunin da sojojin yahudawan suka samu; to sai dai a fili yake cewa damuwar da sojojin yahudawan yahudawan ke ciki ba wai nadamar laifukan da suka aikata kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba ne, musamman mata da kananan yara, sai dai saboda munanan raunuka da ba a taba ganin irinsu ba a sakamakon turjiya.

Tashin hankali da ke tattare da rundunonin sojan Yahudawa, musamman a tsakanin matasa, ya fi fitowa fili fiye da sauran hafsoshi da sojoji na mulkin mamaya. A kan wannan batu, wani marubuci Bayahude kuma kwararre kan matsalar tabin hankali "Ravital Hofil" ya buga wata makala da ke yin nazari game da raunin tunani na sojojin Yahudawa waɗanda ke aiki a kai a kai a matsayin dakarun ajiyar sojojin mamaya.

Wani sashe na wannan makalar yana cewa: Sojojin sun yi tunanin cewa bayan shekaru uku na cutar ta Corona, sojojin sun shirya tsaf; amma kwatsam sai yaki ya barke sai muka ga yanayin da ya gagara shawo kan lamarin. Baya ga asarar rayuka da ake ci gaba da yi ga sojojin Isra'ila, illar da wannan yakin ya haifar yana da yawa, har ma wadanda suka tsira suna ganin cewa rayuwarsu ta kare.

Yael Frocher, tsohon shugaban sashen kula da tabin hankali na sojojin Isra'ila ya yi kashedin cewa: "Sojojin ajiyar suna fuskantar kasada da yawa, da suka hada da lalata ayyukansu da rayuwar danginsu, keɓe kansu, da kuma abubuwan da suka faru da suke faru sakamakon yaƙi."

Masanin ilimin halayyar dan Adam Rona Ackerman na Isra’ila ta ce yaki yana barin tabo da za a iya gani da kuma barnar tunani da ke dadewa, musamman a tsakanin sojoji, domin dole ne su nuna karfinsu, don haka da wuya a gane raunin da ya bayyana a ruhinsu; har ta kai ga cutar da kansu kuma da yawa daga cikin wadannan sojoji sun kashe kansu.

A cikin wani rahoto da aka tace game da kididdigar kisan kawuka a cikin sojojin Isra'ila, tashar Kan Isra'ila ta ce sojojin Isra'ila 16 ne suka kashe kansu tun daga farkon shekarar 2025. A cikin 2024, an sami rahoton kisan kai 21 a cikin sojojin Isra'ila, wanda ya kai 17 a cikin 2023.

Your Comment

You are replying to: .
captcha