15 Yuni 2025 - 23:12
Source: ABNA24
Daily Telegraph: Makamai Masu Linzami Na Iran Sun Rugujetsarin Tsaron Saman Isra'ila

Jaridar The Daily Telegraph ta Burtaniya ta tabbatar da cewa tsarin tsaron sararin samaniyar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya durkushe sakamakon dimbin sabbin makamai masu linzami na Iran.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti ta kasa da kasa ABNA ya habarta cewa: jaridar The Daily Telegraph ta kasar Britaniya ta bayyana cewa, manyan naurorin tsaron sararin samaniyar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun durkushe bayan saukar dimbin makamai masu linzami na Iran.

A wani sabon zagaye na harin makami mai linzami da Iran ta kai kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, wanda shi ne kashi na biyu cikin kasa da sa'o'i 2, an harba makamai masu linzami fiye da 30 zuwa yankunan da aka mamaye, musamman birnin Haifa. Sa'a guda da ta gabata an harba makamai masu linzami sama da 50 a yankuna daban-daban na gwamnatin Isra'ila ciki har da Tel Aviv.

Majiyoyin yahudawan sahyoniya sun sanar da cewa an kai hari ga wasu muhimman wurare.

A yayin shirye-shiryen sojojin Isra'ila na yiwuwar kai hare-haren makamai masu linzami na Iran, baya ga tsarin tsaron Isra'ila masu yawa, na'urorin kariya daga makamai masu linzami daga Amurka da kasashen Turai suna cikin shirin ko ta kwana a ciki da wajen yankunan da aka mamaye domin dakile makamai masu linzami na Iran. Haka kuma wasu gwamnatocin kasashen Larabawa ciki har da kasar Jordan suna ci gaba da kokarin kakkabe makamai masu linzami na Iran da kuma hana su shiga sararin samaniyar yankunan da aka mamaye.

Your Comment

You are replying to: .
captcha