14 Yuni 2025 - 14:23
Source: ABNA24
Munanan Hare-Haren Mkamai Masu Linzami Da Iran Ta Kai Wa Isra'ila

Iran: Yakin zai fadada a cikin kwanaki masu zuwa kuma dukkanin yankunan da aka mamaye da sansanonin Amurka a yankin suna cikin hadafin. Masu zalunci za su biya farashi mai tsada.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: majiyoyin jami’an gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayar da rahoton mutuwar ‘yan sahayoniya hudu tare da raunata wasu 200 sakamakon harin makami mai linzami da Iran ta kai. An gudanar da wannan farmakin ne a matsayin somin tabin martani ga gagarumin farmakin da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan kasar Iran a jiya Juma'a.

A cewar rahotanni daga tashar Kan da Channel 12 na Isra'ila, Iran ta harba makamai masu linzami kusan 200 a wurare daban-daban a tsakiya da arewacin Isra'ila tun a daren jiya. Wasu daga cikin wadannan makamai masu linzami sun auna garuruwan Rishon Lezion da Ramat Gan kusa da Tel Aviv.

Jami'an Isra'ila sun tabbatar da cewa an kashe mutane uku a Rishon Lezion da wani mutum guda a Ramat Gan. A sa'i daya kuma, tashar tashar 13 ta Isra'ila ta ba da rahoton barna mai yawa a yankin babban birnin Tel Aviv, inda ta rubuta cewa gine-gine da ababen hawa da dama sun lalace.

A cewar jaridar Haaretz, gine-gine tara a Ramat Gan sun lalace gaba daya sannan an kwashe mazauna yankin 300 daga yankin. Ita ma wani hasumiya mai hawa 32 da ke Tel Aviv ta samu mummunar barna.

Shugaban ‘yan sandan Tel Aviv ya bayyana hare-haren a matsayin wani babban lamari ne da ya shafi wurare da dama. Ya kara da cewa: "Wasu makamai masu linzami sun lalata dukkan benayen wani gini, kuma har yanzu kungiyoyin agaji na kwashe mutanen da suka makale a matsuguni".

Ci Gaba Da Arangama Da Barazanar Zafafa Hare-Hare

Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa, an ci gaba da kai hare-haren na Iran a safiyar yau, kuma dakarun tsaron sun yi nasarar dakile wasu jiragen sama marasa matuka a yankin tekun Nahril Mayyit, da tsaunukan Hebron, da kwarin Arabah, da tashar jiragen ruwa na Eilat.

A gefe guda kuma, gidan talabijin na Isra'ila ya bayar da rahoton cewa, wani makami mai linzami ya kai wani muhimmin wuri a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a wasu sassan tsakiyar kasar. Asibitin Wolfson da ke Tel Aviv ya kuma bayar da rahoton karbar mutane 21 da suka jikkata, daya daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

Aikin Alkawari Na Gaskiya Karo Na  3

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun sanar da cewa, aikin kai harin mai taken Tabbataccen Alkawari Na 3 an gudanar da shi ne a matsayin mayar da martani kai tsaye ga hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama tare da yin amfani da ingantattun makamai masu linzami da kuma Makamai masu ci gaba.

Kakakin sojin Iran ya yi gargadin cewa a harin na gaba, za a harba makamai masu linzami 2,000 a lokaci guda, wanda zai ninka har sau 20 na harin yanzu.

Har ila yau Iran ta sanar da kakkabo jiragen leken asirin haramtacciyar kasar Isra'ila a yankuna irin su Salmas, Urmia, Ardabil da Marivan, sannan ta jaddada cewa ta kakkabo wasu jiragen yaki marasa matuka guda biyar.

Majiyar sojojin Iran ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Fars cewa: yakin zai fadada a cikin kwanaki masu zuwa kuma dukkanin yankunan da aka mamaye da sansanonin Amurka a yankin suna cikin hadafin. Masu zalunci za su biya farashi mai nauyi.

Bayan wadannan hare-hare, an yi ta jin karan sautin kararraki a daruruwan wurare da suka hada da Kudus, Tel Aviv da matsugunan Isra'ila a gabar yammacin kogin Jordan, kuma gwamnatin Isra'ila ta ci gaba da yin shirin taka tsantsan.

Wani babban jami'in Iran ya kuma shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa: "Babu inda Isra'ila ke da aminci kuma wannan martanin farko ne kawai".

Your Comment

You are replying to: .
captcha