Bari mu kalli jiragen ruwa guda biyar, a lokuta 5 mabanbanta, wadanda suka cikin teku da manufa daya: karya shingen da aka yi wa Gaza. Na farko shine a shekarar 2010. Shahararren jirgi mai suna Mavi Marmara.
Ya taso ne daga Turkiyya tare da masu fafutuka 700 daga kasashe 40 daban-daban tare da taimakon magunguna da na abinci, amma a cikin ruwan kasa da kasa, sojojin Isra'ila sun kai hari a kansa tare da kashe mutane 9. Inda Duniya ta kadu kuma Turkiyya ta yanke huldar ta da Isra'ila.
A lokaci guda kuma, "Jirgin 'Yanci" ya zama alama ta duniya na gwagwarmayar jama'a kuma wannan ya zo da biyan farashi mai tsada ga gwamnatin Isra'ila, wacce ba ta bin kowace doka. Bayan shekara guda, jirgin na biyu ya shirya don tafiya.
Amma a wannan karon, ba wai harin soji ne suka dakatar da shi ba, a’a ta hanyar matsin lamba na diflomasiyya ne. Kasar Girka ba ta bar sa ya motsa daga tashar jiragen ruwan ta ba. Sai aikin bai yi nasara ba, amma ba a yanke tsammani da shii ba.
A cikin 2015, wani jirgin ruwa na Sweden mai suna Marian ya tashi. Har ila yau, Isra'ila ta tare shi a cikin ruwan kasa da kasa kafin ya isa. A wannan karo, ba tare da zubar da jini ba.
Amma sakon ya fito fili karara: tekuna suma suna cikin takunkuman shingaye, kuma kasashen da ke magana kan 'yanci da 'yancin dan adam sun yarda tare da amincewa da wannan katangewar.
A cikin 2018, jirgi na huɗu, mai suna "Komawa," ya tashi zuwa Gaza. Isra'ila ta kama wadanda suke acikinsa ta hanyar sanya masu shokin wutar lantarki da tare da kamasu.
A wannan shekara, wani motsi na babbar alama ya fara a watan Mayu, Amma shima a wannan karon an dakatar da shi da wulakantacciyar hanya.
Labarin shi ne cewa a safiyar ranar 2 ga Mayu, 2025, wani jirgin ruwa daga "Gaza Freedom Flotilla", dauke da mutane 16 zuwa 30 masu fafutukar kare hakkin bil'adama na kasa da kasa da kuma taimakon jin kai ga mutanen Gaza, wani jirgin mara matuki ya kai masa hari a cikin ruwa na kasa da kasa kusa da Malta.
Har yanzu dai ba a fayyace b hakikanin lamarin ba, kuma ko shakka babu a bayyane yake, su wane ne ke da alhakin wannan harin, kuma har yanzu an yi shiru da wannan lamari.
Amma a yanzu, jirgin "Madeleine", wanda kungiyar Freedom Flotilla Coalition ta shiryawa tafiya, yana kan hanyar zuwa Gaza don kai kayan agaji ga yankin.
Jirgin "Madeleine", wanda ya bar Catania, Sicily, a ranar 1 ga Yuni, 2025, zuwa zirin Gaza, yana dauke da masu fafutuka na duniya 12, ciki har da Greta Thunberg: mai fafutukar kare muhalli ta Sweden; Liam Cunningham: ɗan wasan Irish; Rima Hassan: 'yar majalisar Turai daga Faransa; Yasmine Achar: Jamus mai fafutukar kare hakkin bil'adama; Tiago Avila: Bafalasdine mai fafutuka daga Brazil; Omar Fayyad: Dan jaridar Faransa.
Eh, aƙalla sau biyar yanzu, mutane daga sassa daban-daban na duniya sun yanke shawarar tafiya hannu rabbana zuwa ɗaya daga cikin mafi tsaurin wuri a duniya. Ba tare da sojoji ba. Ba tare da takunkumi ba. Kawai ta jirgi da jirgin ruwa. Kuma watakila kawai tare da lamirin zuciyarsu.
Haka yake a wannan karon. Ko ba komai wannan jirgin ruwan ya isa Gaza ko bai isa ba, abin da ke da muhimmanci shi ne duniya ta fahimci cewa watakila duniya zata iya farkawa, watakila har ta iya yin wani abu.
Sunana Greta Thunberg kuma ni ƴar Sweden ce Idan kun ga wannan bidiyon An kama mu an yi garkuwa da mu
A cikin ruwan ƙasa da ƙasa na duniya Ta hannun sojoji ma'aikatan Isra'ila, Ko sojojin da ke goyon bayan Isra'ila.
Sojojin Isra'ila sun kwace jirgin ruwan Madleen da ke dauke da tutar Burtaniya. kafin ya isa Gaza da kayan agajin jin kai.
Jirgin ruwan wanda ya tsaya kimanin mil 100 daga gabar tekun, yana ɗauke da mutane 12 ciki har da 'yar gwagwarmayar Sweden Greta Thunberg da MEP ta Faransa Rima Hassan.
Jirgin ruwan ya yi nufin haskaka rikicin jin kai na Gaza amma kwamandojin Isra'ila sun kama shi a cikin ruwan kasa da kasa.
An tsare ma'aikatan, kuma jirgin ya koma tashar jiragen ruwa da ke karkashin ikon Isra'ila.
Jirgin Madleen yana a ɗauke da muhimman taimakokamar shinkafa da madarar jarirai.

Your Comment