3 Yuni 2025 - 22:15
Source: ABNA24
Hamas Ta Kashe Tare Kama  Sojojin Isra'ila A Shuja'iyyah

Kafofin watsa labarai sun tabbatar da aukuwar mummunan tarko ga sojojin Isra'ila a gabashin Gaza wanda ya haɗa kashewa da kama wasu tare da jikkata wasu da dama daga cikin sojojin 

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa: Kafofin yada labarai na yaren yahudanci sun sanar da cewa an jikkata wasu sojojin Isra'ila a wani tarko a unguwar Shuja'iya da ke gabashin Gaza.

Wasu majiyoyin labarai sun kuma jaddada cewa jirage masu saukar ungulu na sojojin Isra'ila zuwa yanzu suna ta yin jigilar sojoji da suka samu raunuka daga Gaza zuwa asibitocin birnin Kudus da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran Ibrananci mai suna Security News daga filin daga ya bayar da rahoton cewa, a wani mummunan yanayi na tsaro a Shuja'iyah, an kashe wani sojan Isra'ila tare da jikkata wasu da dama.

Kamfanin dillancin labaran Quds Network cewa, sojojin gwamnatin mamaya na kwashe matattu da kuma wadanda suka jikkata daga yankin bayan da dakarun gwagwarmaya suka yi musu kwanton bauna a gabashin unguwar Shuja'iya da ke birnin Gaza.

An samu nasarar kame sojojin yahudawan sahyoniya a unguwar Shujaiyeh

Tashar Hadshot ta bayar da rahoton nasarar da Hamas ta yi na kame sojojin Isra'ila.

Your Comment

You are replying to: .
captcha