A yayin cika shekaru 36 da wafatin Imam Khumaini (RA) Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa;
A safiyar yau a wani gagarumin taro mai cike da buunkasa da jama'a suka gudanar a hubbaren Imam Khumaini (RA) Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da irin tasirin da juyin juya halin Musulunci ya haifar na ci gaban da ke faruwa a duniya a yau: Marigayi Imam tare da taka tsantsan da hankali da ya samo tushe daga imani, ya kafa tushen ci gaba da yunkuri mai karfi da daukaka na juyin juya halin Musulunci na asali mai suna "'yancin Al’umma" na wannan kasa ta asali da mahangar juyin juya halin Musulunci. Masoyiyar kasarmu Iran bisa dogaro da wannan tsuhen, ta kai ga jin dadin jama'a, tsaro mai dorewa, da kara kyautata matsayinta na kasashen waje da makoma mai haske.
A yayin da yake bayani kan batun nukiliyar kasar, Ayatullah Khamenei ya kuma bayyana cewa Iran ta mallaki cikakken tsarin makamashin nukiliya da ake alfahari da shi, sakamakon imani da al'ummar kasar da matasan masana kimiyya suka yi na sanya cewa "zamu iya". Yayin da yake ishara da irin muhimman tasirin da wannan masana'anta ke da shi kan ci gaban sauran ilimomi da masana'antu, ya yi la'akari da shirin nukiliyar da Amurka ta gabatar a matsayin wanda ya saba wa ka'idar cewa "za mu iya", ya kuma jaddada cewa: Babbar masana'antar nukiliya ba tare da wadatuwa ba a zahiri ba ta da wani amfani, kuma ya kamata Amurka da gwamnatin Sahayoniya su san cewa ba za su iya yin komai ba wajen cimma babbar manufarsu ta hana kera nukiliya ba.
Haka nan kuma ya dauki Imam Khumaini a matsayin babban mai tsara babban tsarin ginin kasar tsayayye da iko na Jamhuriyar Musulunci yana mai cewa: Shekaru talatin da shida bayan wafatin wannan mai girma, kasancewarsa da tasirin juyin juya halinsa suna nan daram tare d akaruwa a cikin lamurra da suka hada da samun rushewar manyan kasashe masu iko, da samuwar tsarin kasa da kasa, da koma bayan matsayi da tasirin da Amurka take da shi, da bullowar kiyayya daga al'ummomin kasashen yammaci ga Sahyuniyanci, harma a kasashen Turai da Amurka, da ma bayyanar yunkurin da yawa daga Al’ummomi wajen farkawa da yin watsi da manufofin yammacin Duniya.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin shan mamakin da kasashen yammacin duniya suka yi na fuskantar "Rundunar al'ummar Iran bisa jagoranci wani malamin addini, da nasarar da Imam da al'ummar Iran suka samu wanda basu da komai a hannunsu a kan gwamnatin Pahlawi masu dauke da makamai, da kawar da kasantuwar ma'abota girman kai da nade tabarmar kunyar Amurkawa da yahudawan sahyoniyawa masu cin banza masu kwashe dunkiyar al’umma daga Iran". Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: shan mamaki na biyu shi ne kafa tsarin jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da bibiya kulawar Imam.
Haka nan kuma yayin da yake tunawa da fatan Amurkawa na samun gwamnatin sulhu a kasar Iran da kuma tabbatar da haramtattun manufofinsu a kasar, Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Imam ta hanyar bayyana matsayarsa a fili kan tabbatar da tsarin Musulunci da na addini a kasar Iran, ya yi watsi da wannan fata na Amurkawa, kuma daga nan ne makirce-makircen makiya suka fara kai hari. Haka nan kuma ya kira girma da bambance-bambancen da tsananin tsare-tsaren rugujewar kasashen yamma musamman Amurka kan juyin juya halin Musulunci da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin juyin juya halin Musulunci, ya ce: Tunzura kabilanci, ba da makamai ga masu adawa da juyin juya hali na hagu, tunzura da goyon bayan kyarkeci mashayin jini da ake kira Saddam mai kishirwa da kai wa Iran hari da kuma kisan gilla ga sahabban Imam na daga cikin yunkurin makiya. Yunkurin kashe mutane a shekaru masu dama tare da kashe masana ilimin Nokliya duka shine aikin makiya. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira "cikakkun takunkumin da ake ci gaba da yi, da harin da sojojin Amurka suka kai kan Tabas, da harin da aka kai kan jirgin saman fasinja na Iran a tekun Fasha" da dai sauran munanan ayyukan makiya ga al'umma da juyin juya halin Musulunci, ya kuma ce: A bayan duk wadannan makirce-makircen, gwamnatoci ne ma'abuta girman kai, musamman ma Amurka da gwamnatin Sahayoniya, da kuma hukumomin leken asiri irin su CIA Amurka, da hukumar leken asirin Birtaniya da Mossad.
Haka nan kuma ya dauki manufar wadannan munanan ayyuka na rusawa da barna a matsayin raunana tsarin Jamhuriyar Musulunci, sannan kuma ya jaddada cewa: Al'umma da tsarinsu sun yi tsayin daka da dukkanin wadannan makirce-makircen, kuma sun dakile makirci fiye da dubu, kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba wai kawai ba ta yi rauni ba ne, a'a tana ci gaba da tafiya da karfi, kuma za ta ci gaba da tafiya cikin izza a nan gaba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya dauki cewa galabar son zuciya a kan hankali a matsayin wani babban bala'i kuma shine babban abin da ke haifar da karkacewar juyin juya hali masu yawa ciki har da juyin juya halin Faransa, yana mai jaddada cewa: Marigayi Imam mai girma tare da hangen nesa na Ubangiji da tunani da hankali da ya samo daga tushen imani da gaibi, ya kare juyin juya halin Musulunci daga wannan bala'i mai halakarwa da kuma ba shi kariya kuma bai bayar da dama na ya zamao ansamu galabar son zuciya akan hankali ba da har zai karkatar da juyin juya halin mutane daga kan tafarkinsa na asali.
Haka nan kuma ya kira tsarin wilayatul fikih da ‘yancin kai na kasa a matsayin shika-shikan biyu na hankali na Imam yana mai cewa: Rukunin Wilayatul fikih yana kiyaye bangaren addini da kuma hana karkatar da juyin juya halin da ya taso daga dalilai da sadaukarwar addini na mutane, haka nan kuma ‘yancin kai na kasa yana kunshe da da dama daga cikin tunani da manufofin Imam.
Ayatullah Khamenei ya dauki ma’anar da wasu suke dauka na cewa 'yancin kai na kasa yana matsayin kadaici da yanke alaka da duniya a matsayin kuskure kuma wani nau'i ne na Mugalada, ya kara da cewa: 'Yancin kasa yana nufin Iran da al'ummar kasarta ta hanyar tsayawa da kafafunta ba tare da dogaro da wasu ba, ba su jira koren haske, ko kuma su damu da jajayen hasken Amurka da makamantansu, sannan kuma su yanke hukunci da daukar matakin da ya dace ba tare da la'akari da yarjewa ko sabaninta ba daga wasu masu ikonn da suke saba da juna ba.
A yayin da yake bayyana ka'ida ta farko da ta samo asali daga maganganun Imam mai girma dangane da batun 'yancin kai na kasa, ya jaddada manufar cewa: "Za mu iya" ya kuma ce: Sabanin gwamnatin azzaluman da ta sanya al'umma su yi imani da cewa ba za mu iya ba, Imam ya farfado da dogaro da kai da kuma cewa da "za mu iya" a matsayin kasa ta Iran da matasa da 'yan siyasa, da kuma ci gaba mai ban mamaki da aka samu a fagagen ilimi, da fasaha da kuma gina kasa.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi la'akari da tsare-tsare na masu mummnan nufi na yin watsi da ruhin "za mu iya" a cikin al'ummar Iran a matsayin wata alama ta irin muhimmancin da ba zai taba misaltuwa ba na wannan ginshiki na ainihi sannan kuma ya lura da cewa: Yanzu a cikin wannan batu na nukiliya da kuma tattaunawar da ake yi tare da shiga tsakani na Oman, shirin da Amurkawa suka gabatar ya kasance yana adawa da ginshikin "za mu iya" 100%.
Ya kira ka'idar '' Gwagwarmaya'' da ma'anar aiki da imani da rashin kaskantar da kai a gaban son rai, tilastawa, da cin zarafi na manyan kasashe a matsayin wani bangare na 'yancin kai na kasa sannan kuma ya jaddada "inganta karfin tsaro" a matsayin wata manufar ta daban ya ce: A farkon juyin juya hali karfinmu wajen samar da tsaro ya kasance dan kadan kuma yana kusa da sifili ma, amma tare da karfafawa da kuma ba da himma ta Imam tsaro, a yau aikin karuwar ikon tsaro da kariya ya fara ta yadda Kasashe masu karfin fada aji sun amince da matsayin Iran na farko a yankin a wasu nau'ikan tsaro, ko kuma sun bayyana mamakin wasu karfin Iran din duk da takunkumin da aka kakaba mata.
Ka'idar Tushen "Bayyanawa" wani bangare ne na tsarin tunani ilimi da aiki na Imam wajen tabbatar da 'yancin kai na kasar Iran, wanda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da shi da cewa: "Tun farkon yunkuri na shekarar 1962 har zuwa shekarar karshe ta rayuwarsa, Imam yana bayyana muhimman batutuwa ga al'umma, wanda ya zamo rubuce-rubucensa a shekarar karshe, wadanda ya fuskanci mutane da maganarsa, da makarantun hauza, da malaman jami’a suna daga cikin wadanda yake nufa da rubuce-rubucensa, Tabbas bayanin Imam bai dogara ga yin bayani kawai ba, a'a, yana gamsar da kafa hujja ta hankali da tunani, yana magana da zukata da tunani a lokaci guda.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da wani bangare na jawabin nasa wajen yin bayani kan batun nukiliyar kasa da kuma bayyana batutuwan da suka shafi wayar da kan al'umma, ya kuma ce: Iran ta samu ci gaba da cin moriyar makamashin nukiliyar cikkaken tsarin makamashin nukiliya sakamakon irin basirar matasanta da kuma kokarin masana kimiyya masu kokari, yayin da akwai kasashe kalilan a duniya da suke da wannan damar.
Bai dauki fa'idar da masana'antar nukiliya ke da shi ba ta takaita ne ga samar da wutar lantarki mai tsafta da arha ba kawai, yana mai karawa da cewa: Masana'antar nukiliya uwa ce kuma babbar masana'anta, kuma a cewar rahotanni daga masanan kimiyya ya kamata a gabatar wa jama'a, fannoni daban-daban na kimiyya da injiniyanci kamar kimiyyar nukiliya, injiniyancin makamashi, injiniyancin kayan aiki, da kuma daidaitattun fasahohi masu mahimmanci a cikin kayan aikin likitanci, sararin samaniya, da madaidaicin abubuwan da suka dogara da masana'antar nukiliya ko na'urori masu auna firikwensin, abin da ya shafi na'urorin lantarki ko masana’antar nukiliya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana fa'idar da masana'antar nukiliya ke da shi a bangaren likitanci da magunguna wajen tantance ko magance munanan cututtuka, da kuma tasirin wannan masana'antu a masana'antu da suka shafi aikin gona da muhalli da sauran fannonin da suka dace, ya ce: A cikin masana'antar nukiliya, inganta makamashin Uranium wani muhimmin lamari ne mai tushe kuma muhimmin batu da makiyanmu ma suka tabo kan wannan batu.
Da yake bayyana dalilin da ya sa babbar masana'antar nukiliyar ba ta da wani amfani ba tare da karfin ingantawa ba, ya ce: Ba tare da wadata ba, dole ne mu tuntubi masu shi don samar da mai don samar da wutar lantarki; Kamar yadda yake gaya mana cewa duk da cewa muna da man fetur, ba mu da ikon gina matatun mai da kuma samar da mai don haka dole ne mu bi bukatun wasu kasashe na saye da samar da mai.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa: Ba tare da wadatuwa da kuma yiwuwar samar da man fetur ba, ko da an mallaki tashoshin makaman nukiliya 100 ba shi da wani amfani; saboda dole ne mu tuntubi Amurka don samar da mai, kuma za su iya gindaya sharudda da dama don haka, kamar yadda aka samu a shekarun 1980 na samar da kashi 20 cikin dari.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da batun shiga tsakani na wasu kasashen abokantaka na Iran guda biyu bisa bukatar shugaban kasar Amurka na wancan lokacin na mika wani kaso 3.5 na kayan wadata da su domin samun kashi 20 cikin 100 na man fetur don biyan bukatun cikin gida, sai ya ce: A lokacin ne jami'ai suka amince da musayar, na ce dayan bangaren ya mika wa Bandar Abbas man kashi 20 cikin 100, mu kuma za mu aiwatar da musanyar ne bayan gwaji, amma a lokacin da suka ga jajircewarmu akai sai suka karya alkawarinsu, kuma ba su yi bayar da kasha 20 na man.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Tabbas a yayin wannan fadace-fadacen siyasa masana kimiyyar mu sun samar da kashi 20 na makamashin man a cikin gida.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira kalaman farko da bukatun Amurkawa kan batun nukiliyar Iran shine haramtawa Iran gaba daya daga wannan masana'anta da kuma fa'idojinta iri-iri ga al'umma, da kuma samar da rashin aikin yi da yanke kauna na dubban matasa masu bincike da masana kimiyya, inda ya ce: Shugabannin Amurka masu rashin kunya da girman kai suna maimaita wannan bukata cikin harsuna daban-daban.
Ya dauki hakikanin abin da Amurka ke da shi na tilastawa a matsayin adawa da ci gaba da wadatuwar al'ummar Iran tare da jaddada cewa: Mun bayyana wadannan gaskiyar ne domin al'ummar Iran su san halin da ake ciki daidai gwargwado; su ma jami'an wajibi ne su yi karin bayani.
Ayatullah Khamenei yana mai jaddada cewa: " Martaninmu a bayyane yake kuma sannance game da hayaniya na gwamnatin Amurka da rikon sakainar kashi" Ayatullah Khamenei ya tuno da gazawar wani shugaban Amurka a 'yan shekarun da suka gabata, yana mai bayyana cewa idan har zai iya, zai sassautawa masana'antar nukiliyar Iran din, ya kuma kara da cewa: "A yau, dunkulewar masana'antarmu ta nukiliya ta zama mafi tsanani, kuma kamar yadda ya ce ba zai iya yin komai ba, su ma masu mulki yanzun su sani cewa ba za su iya yin wani tsautsayi ba a cikin wannan lamarin”. Ya yi la'akari da maganar farko da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi wa Amurkawa da sauran masu adawa da masana'antar nukiliyar Iran a matsayin tambaya kan tushen da'awarsu ta fuskar shari'a, sannan ya ce: "Maganarmu gare su ita ce, al'ummar Iran na da zabin ta, me kuke yi kuma daga wane matsayi kuke tsoma baki a kan ko muna da wadata ko a'a? A bangare na karshe na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da laifukan ban mamaki da rashin imani da gwamnatin sahyoniyawa take yi a zirin Gaza, inda suke afkawa jama'a ta hanyar kafa wata cibiyar raba abinci inda ya ce: Wannan matakin ya kai kololuwar kaskanci, da fasikanci, da zalunci, da tabewa na munanan ayyuka, hakika abin mamaki ne.
Ya kira Amurka a matsayin mai hannu a laifukan gwamnatin sahyoniyawan ya kuma kara da cewa: Don haka ne muka dage cewa dole ne Amurka ta fice daga wannan yanki.
Ayatullah Khamenei ya kira aikin gwamnatocin Musulunci da cewa mai nauyi ne, ya kuma jaddada cewa, a yau ba lokacin yin la'akari da kiyaye aiki ba ne, da nuna tsaka-tsaki ba, da yin shiru. Ya kara da cewa: Idan har wata gwamnatin Musulunci tana goyon bayan wannan gwamnati ta kowace fuska ko ta kowace hanya, ko ta hanyar daidaita alaka, ko rufe hanyoyin taimakawa al'ummar Palastinu, ko kuma tabbatar da laifukan sahyoniyawa, to ta sani tabbas kunya ta har abada za ta ci gaba da kasancewa a goshinta.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya dauki hukuncin Ubangiji da na lahira na yin hadin gwiwa da yahudawan sahyoniya a matsayin mai tsanani mai tsanani da kuma nauyi, sannan ya kara da cewa: Tabbas ko a nan duniya al'ummomi ba za su manta da wadannan ha'inci ba; haka nan dogaro da gwamnatin sahyoniyawan ba ya samar da tsaro ga kowace gwamnati domin kuwa wannan gwamnati tana kan rugujewa ne da hukumcin Ubangiji, kuma in sha Allahu ba za a dade ba.
Har ila yau, Ayatullah Khamenei ya dauki ranar Arafa a matsayin mabubbugar addu'a, kaskantar da kai, mai da hankali da kuma addu'a, ya kuma shawarci al'umma musamman matasa da su yi amfani da damar Arafat da karanta addu'ar kauna ta Imam Husaini (AS) a wannan rana, da addu'a ta 47 na Sahifa Sajjadiya gwargwadon ikonsu, da kuma neman tsarin Allah.
A farkon wannan taro, Hujjatul Islam Walmuslimiin Sayyid Hasan Khumaini sun kira juyin juya halin Musulunci mafi shaharar juyin juya hali a tarihi inda ya ce: Daukaka ita ce mai gina al'umma, kuma a ko da yaushe mu yi taka tsantsan cewa, bisa la'akari da yadda Imam mai girma kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da nanata cewa "Daukakar Musulunci" da "Daukakar kasa" ba zasu taba raunana ba ta ko wace hali.
Sayyid Mai kula da haramin Imam Khumaini ya yi la'akari da farkawa da tsayin dakan da juyin juya halin Musulunci ya haifar a kasashen Lebanon, Iraki, Yemen da Palastinu da muhimmanci, ya kuma soki shirun da wasu kasashe suka yi wajen fuskantar laifuffukan da gwamnatin yahudawa suke yi a Gaza inda ya ce: "A yau muryar Imam tana cikin kunnuwan kowa da kowa cewa dole ne a shafe Isra'ila da kuma halakar da ita saboda ita ciwon daji ce".
Your Comment