26 Mayu 2025 - 17:32
Source: ABNA24
Ƙasashen Duniya 32 Na Yunƙurin Yin Tattaki Zuwa Gaza

Haɗin gwiwar ƙungiyoyi, ƙungiyoyi masu goyon bayan Gaza da cibiyoyin shari'a na duniya daga ƙasashe 32 na duniya sun fara ƙaddamar da wani aiki mai suna "Tattakin Duniya Zuwa Gaza" don nuna rashin amincewa da mummunan halin jin kai a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa: Mahalarta gangamin, wadanda galibi sun fito ne daga kasashen yammacin duniya, sun fito ne daga kasashe daban-daban, kabilu, addinai da kuma kungiyoyi daban-daban.

Adadin mahalarta tattakin zuwa yanzu ya riga ya wuce 10,000, kuma ƙungiyoyin aiki daban-daban suna bibiyar yanayin da ake da su don bincikar dabaru da sadarwar kafofin watsa labarai a cikin dukkan harsuna da kuma rarraba hanyoyin da tafiyar zata gudana.

A wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba, hadaddiyar kungiyoyin kare hakkin bil adama, kungiyoyi da kungiyoyin hadin kai daga kasashe 32 na duniya sun sanar da kaddamar da shirin "Tattakin Duniya Zuwa Gaza". Wannan matakin na da nufin karya kawanyar da Isra'ila ta yi wa zirin Gaza na tsawon watanni 20 da kuma mayar da martani ga mummunan halin jin kai da ake ciki a yankin.

Saif Abu Kashk shugaban kungiyar hadin kan duniya da ke yaki da mamayar Isra'ila, ya shaidawa tashar talabijin ta Aljazeera cewa, babban makasudin wannan tattakin shi ne a dakatar da kisan kiyashin da ake yi, da ba da damar kai agajin jin kai cikin gaggawa, da kuma kawo karshen killace Gaza da zaluncin da Isra'ila ke yi.

A cewarsa, ya zuwa yanzu sama da mutane 10,000 daga kasashe daban-daban ne suka bayyana shirinsu na shiga wannan aiki. Mahalarta taron sun fito ne daga al'ummomi daban-daban, musamman kasashen yammacin duniya, ba wai kawai na Larabawa da na Musulunci ba. Wannan motsi yana biye da haɗin kai tsakanin ƙungiyoyi da fassarar harsuna da yawa don yin tasiri ta fuskar watsa labarai da dabaru.

Daga cikin muhimman manufofin wannan tattaki har da kai kayan abinci da magunguna da man fetur cikin gaggawa zuwa Gaza ta mashigar Rafah, inda a halin yanzu aka dakatar da dubban manyan motoci dauke da muhimman kayan agaji.

Bugu da kari, masu shirya taron suna kira da a kawo karshen killace Gaza da kuma kafa wata hanya mai dorewa ta jin kai domin shigar da muhimman kayayyaki kamar abinci, ruwa da magunguna ba tare da wani sharadi ba.

Har ila yau gangamin na neman tona asirin yin shuru da hadin kai da wasu gwamnatoci ke yi a cikin laifukan gwamnatin sahyoniyawa ta hanyar wawitar da hankalin al'ummar duniya. An kuma yi kira ga majalisun dokoki da ‘yan siyasa da su matsa wa gwamnatocinsu lamba domin su dauki matakin gaggawa.

A cewar lauyan Jamus Melanie Schweitzer, zanga-zangar ta zaman lafiya ce kuma ba ta da goyon bayan wata hukuma. Mahalarta taron sun fito ne daga sassa daban-daban na rayuwa, tun daga likitoci da masu fafutukar kare hakkin bil adama har zuwa ’yan kasa na kasa da kasa masu shekaru daban-daban da ke biyan bukatun kansu.

Kamar yadda aka tsara, mahalarta taron za su fara isa birnin Alkahira sannan su tafi birnin Arish. Daga nan ne za a fara tattaki da ƙafa zuwa mashigar Rafah. Za a fara yunkurin ne a ranar 12 ga watan Yuni.

Dangane da haka, ana ci gaba da gudanar da aiki tare da ofisoshin jakadancin Masar da sauran cibiyoyin hukuma a kasashe daban-daban.

Wannan kamfen, tare da wasu tsare-tsare irin su ayarin motocin "Samoud" da kuma kawancen "Freedom Flotilla", ana shiryawa da kuma hada kai don cimma burin bai daya na kawo karshen killace Gaza nan take.

Your Comment

You are replying to: .
captcha