ABNA24 : Iyakokin kasar na kan tudu da aka amince a bude, sune na Seme da ke Lagos zuwa Kwatano, da kuma ta Ilela da ke kan iyakar Sokoto da Jamhuriyar Nijar, sai kuma ta Maigatari da ke kan iyakar jihar Jigawa da Jamhuriyar Nijar, sai kuma ta Mfun da ke kan iyakar Kudu Maso Kudu.
Sai dai Shugaba Buhari ya halarci taron ne ta bidiyo daga gidan sa dake Daura inda ya ke hutun mako daya. Kuma za’a bude sauran iyakokin kafin nan da ranar 31 Ga Disamba shekara ta 2020.
Wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da shugaban yake fuskantar suka mai tsanani game da sace daliban makarantar kwana ta garin kankara su 333 da yan bindiga suka yi .
342/