ABNA24 : Yan dabar dauke da sanduna da adduna da wukake sun mamaye ginin “ Arewa Hause” da ke jihar Kaduna inda ake gudanar da taron lokacin da kungiyoyin suka kira taron manema labarai kafin fara taron, inda suka afkawa Mahalarta taron kuma suka tarwastasu, tare da lalata kujeru da tebura da kuma farfasa gilasan motocin da aka ajiye a harabar wajen.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar ta CNG Balarabe Rufa’i a cikin wata sanarwa da ya fitar ya yi tir da wannan hari da yan Ddaban suka kai tare da bayyanasu a matsayin makiya Arewacin kasar, kana ya nuna cewa babu abin da zai hana su ci gaba da bayyana ra’ayinsu game da halin da yankin na Arewa yake ciki, na tabarbarewar tsaro.
342/