25 Yuli 2016 - 20:13
Iyalan Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu A Juyin Juya Halin Tunusiya Sun Bukaci A Yi Musu Adalci

Al'ummar Tunusiya sun gudanar da zanga-zangar lumana da nufin bayyana rashin amincewarsu da duk wani shirin sakin jami'an tsaron kasar da suke da hannu a kisan 'ya'yansu a lokacin yunkurin juyin juya halin kasar a shekara ta 2011.

Rahotonni daga Tunusiya suna bayyana cewa: Jama'ar kasar musamman iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin yunkurin juyin juya halin da al'ummar Tunusiya suka gudanar da nufin kawo karshen mulkin kama karyar Zainul-Abideen Bin Ali a shekara ta 2011 sun gudanar da zanga -zangar lumana a yau Litinin suna rera taken jaddada rashin amincewarsu da duk wani matakin sakin jami'an tsaron tsohuwar gwamnatin kasar da suke da hannu a aiwatar da kisan gilla kan 'ya'yayensu. 

Masu zanga-zangar sun kuma jaddada yin  kira ga gwamnatin Tunusiya mai ci kan ta hanzarta gurfanar da jami'an tsaron hambararriyar gwamnatin Bin Ali da suke da hannu a kasashe al'ummar kasar a lokacin boren neman kawo karshen mulkin kama karya a Tunusiya.

Yunkurin kifar da gwamnatin kama karya ta Zainul-Abideen bin Ali a Tunusiya ta hanyar boren al'umma ya kai ga samun nasara ne a ranar 14 ga watan Janairun shekara ta 2011, bayan da ya tsere zuwa kasar Saudiyya, kuma yawan masu boren da suka rasa rayukansu sun haura 340 mafi yawansu matasa tare da jikkatan wasu fiye da 4000.