Birtaniya zata sake tattaunanwa da kasashen Afrika kan sabunta huldar kasuwanci tsakaninsu.
Babbar barazana ga kasashen Afrika bayan ficewar Birtaniya ta shafi kudaden tallafin da Tarayyar Turai ke warewa na raya kasashe masu tasowa wanda Birtaniya na cikin manyan kasashen da ke bayar da kaso mai yawa. Yanzu Birtaniya ba za ta sake ware kudaden tallafin ba na kudi sama da euro miliyan 500.
Kenya na fargaba akan raguwar adadin yawan Fulawar da ta ke shigarwa a Birtaniya, saboda girman kasuwar Turai karkashin yarjejeniyar cinikayya ta Tarayyar Turai.288