Kakakin sojan kasar ta Libya, Milad al-zawy ya fada a yau laraba cewa; Bayan kwanciyar hankali da aka samu na wani dan lokaci, yankin alqawarish da ke yammacin Banighazi ya sake zama filin daga.
al-zawy ya kara da cewa; tun ranar lahadin da ta gabata ne aka batakashi a tsakanin sojoji da kuma 'yan ta'adda, inda ake amfani da manya da matsakaitan makamai.
Sojojin na kasar Libya sun yi nasarar kwace wurare da dama daga hannun 'yan ta'addar kungiyar Da'esh. Sai dai sojojin kasar biyar sun jikkata a cikin kwanakin biyu na fadan.288