27 Afirilu 2016 - 16:08
Ban Ki-Moon Ya Bayyana Damuwarsa Kan Ci Gaba Da Bullar Rikici A Kasar Siriya

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwarsa kan yadda ake ci gaba da samun bullar tashe-tashen hankula a kasar Siriya.

A taron manema labarai da ya gudanar da ministan harkokin wajen kasar Austria a yammacin jiya Talata; Babban sakataren Majalisar Dinkin Duiniya Ban Ki-Moon ya jaddada tsananin damuwarsa kan yadda rikicin kasar Siriya ke ci gaba da daukar sabon salo, yana mai bayyana cewa cewa; Dole ne batun kare rayukan fararen hula ya zame babban bukatar da za a tattauna a yayin zaman tattaunawan neman gudanar da sulhu a kasar ta Siriya.

Har ila yau Ban Ki-Moon ya kara jaddada yin kira ga bangarorin da suke rikicii da juna a kasar ta Siriya da su da su ci gaba da mutunta yarjejeniyar da suka cimma ta dakatar da bude a tsakaninsu saboda rashin mutunta yrjejeniyar zai janyo matsala a kokarin da ake yi na isar da kayayyakin jin kai ga mutanen da rikicin kasar ta Siriya ya galabaita su.288