28 Disamba 2015 - 10:01
Dakarun Iraqi sun kwato Ramadi daga hannun IS

Sojoji Iraqi sun yi nasarar kwato garin Ramadi daga hannun mayakan IS bayan an kwashe kwanaki ana dauki ba dadi tsakanin mayakan da dakarun gwamnati.

Tun a watan Mayun 2014 ne Mayakan IS da ke da’awar Jihadi suka kwarbe Ramadi, kuma kwato garin babban birnin lardin Anbar babbar nasara ce ga gwamnatin Iraqi.

Rahotanni sun ce mayakan na ISIS sun fice daga cikin akasarin gine-ginen da suka mamaye, kamar yadda kakakin rundunar da ke yaki da ta’addanci a kasar Sabah al Numan ya bayyana.

Jami’in ya ce sojojinsu na ci gaba da bi sako-sako don tabbatar da cewar sun tsabtace garin ba sauran mayakan IS da suka rage.

Dubban mutanen Iraqi dai sun fito suna murna a sassan kasar musamman a Bagadaza da Karbala.

Rahotanni sun ce akalla jami’an Iraqi 5 suka mutu yayin da kimanin 93 suka samu raunuka.

Zuwa yanzu dai babu cikakken adadin yawan mutanen da suka mutu a musayar wutar da aka shafe kwanaki ana yi tsakanin IS da dakarun Iraqi.288