2 Agusta 2015 - 09:38
An kama Mutumin dake Daukar Nauyin ‘Yan Boko Haram a Chadi

Jami’an tsaro a kasar Chadi sun kame wani mutum da ake zargin cewa shi ne ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram a cikin kasashen Chadi da Kamaru. Jaridar Cameroon Journal ta nakalto daga wasu majiyoyin tsaro a kasar Chadi cewa, an cafke mutumin mai suna Bana Fanaye da aka fi sani da suna Mahamat Moustafa a ranar Juma’ar da ta gabata, bayan samun bayanan sirri dangane da harkokinsa.

Ruhotanni n acewa  an samu tarin makamai da kuma wayoyin salula masu tarin yawa a gidansa, haka nan kuma an samu katuna na wayar salula na kasashen Chadi, Kamaru, Najeriya da kuma Nijar fiye da 50 a hannunsa, tare da wasu takardu da ke dauke da muhimman bayanai.

Majiyoyin tsaron sun tabbatar da cewa wanann mutum ne ke daukar nauyin ‘yan kungiyar Boko Haram a Chadi da Kamaru, tare da horar da su da kuma ba su kudade da makamai.288