Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti {As} -ABNA- ya kawo maku cewa, a wani zaman nazarin da akai kan shirin fim ɗin "Muawiyah", masana sun yi nazari tare da sukar shirin.Inda hatta fim ɗin Muawiyah ya sabawa ra'ayin Sunna.
Hujatul Islam Dr. Mahdi Farmanian, malami a jami'ar addini da mazhabobi ya bayyana a cikin wannan taron cewa: "A yau, Wahabiyawa sun yi niyyar gabatar da tunanin Usmaniyya kamar yadda Sunni suke tunani ta hanyar amfani da fim ɗin Mu'awiyah." Alhali wannan shi ne tunanin Ibn Taimiyya, Ahlus Sunna ma suna adawa da irin wannan tunanin.
Ya kara da cewa: “Bai kamata malamanmu da dattawan mu su kammala dambarwar makiya ba; Domin Wahabiyawa suna kokarin kunna yaƙi tsakanin Shi'a da Sunna. Yayin da babban bambanci da Yakamata mu fahimta shine banbancin da ke tsakanin Ahlus-Sunnah da Wahabiyawa. Don haka za mu iya tunkarar wannan silsilar Fim ta hanyar yin nuni da sukan malaman Sunna sukai masa.
Farfesan jami'ar ya ce: "Wannan silsilar Fim ta yi kokarin yin riko da tarihin Ahlus-Sunnah, amma kuma ta aiwatar da umarni da son ran ma'aikacinta na Wahabiyawa". Don haka masana tarihi na iya sukar wannan silsila ta hanyar nuna kurakuran tarihi masu yawa a cikin wannan silsilar a cewar majiyoyin Sunna.
Silsilar Fim ɗin Muawiyah ba mahangar Ahlus-Sunnah ba ce.
Dr. Ussam Yahya Imad malamin addinin musulunci na kasar Yemen ya ce dangane da mahangar malaman Sunna akan Mu'awiyah: Shaikh Hassan al-Banna ya kasance mai sabani da Mu'awiyah, Ahmad Siddiq Ammari ya rubuta littafi akan Mu'awiyah, har ma Ibn al-Jawzi wanda Salafiyya ne ya rubuta wani aiki dake raddi ga Yazidu. Wadanda suka kirkiro Fim ɗin Muawiyah ba su yarda da akidar Sunna da Shi'a ba. Don haka za a iya cewa Fim ɗin Mu'awiyah ya samo asali ne sakamakon sabanin da ke tsakanin Iran da Saudiyya ba, a daya bangaren kuma, jerin finafinan Iran suna mai da hankali da bada muhimmanci ga mahangar Sunna.
Wannan masanin ilimin addinin musulunci ya ce: "Ba daidai ba ne a gabatar da fim ɗin Mu'awiyah a matsayin mahangar Ahlus Sunna". Wadanda suka kirkiro fim ɗin Mu’awiya sun dogara ne da ra’ayoyin wadanda suke da shakka kan tarihin Tabari a matsayin tushe a tarihin Ahlus-Sunnah. Tarihin Tabari littafi ne da ba Ahlus-Sunnah kadai ke amfani da shi ba, har ma da ‘yan Shi’a. Wadanda suka kirkiro fim ɗin Muawiyah ba su yi amfani da littattafan Tarikh Tabari da Tarikh Ibn Kathir ba saboda ka'idar da suka gabatar game da Muawiyah a cikin wannan silsilar ta ci karo da wadannan littafai.
Shi dai wannan masanin ilimin addinin musulunci ya ce: Don haka Fim ɗin Mu’awiyah ya saba wa tarihin Tabari, domin kuwa tarihin da aka ambata a kan Mu’awiyah a madogaran tarihi na Ahlus Sunna ba shi da bambanci da tarihin da aka ambata a wajen ‘yan Shi’a.
Fim Ɗin Da Akai Yi Shi Makudan Kudaden Dala Miliyan 100!
Hujjatul Islam "Murtaza Fallah", kwararre kan harkokin yada labarai kuma mai sharhi kan harkokin fina-finai, ya ce: "MBC ce ta shirya shirin Muawiyah, ya kamata a watsa shi shekaru biyu da suka gabata, amma an dage shi saboda zanga-zangar kin amincewa". Kasafin kudin Fim din ya kai dala miliyan 100. Kasashen larabawa sun shiga harkar samar da silsilar fim ɗin da tsare-tsarensa a shekarun baya-bayan nan, kuma a bana aka samar da silsilar Muawiyah ne bisa wasu manufofin da wasu kasashen larabawa suka yi. Amma su ma Ahlus-Sunnah ba su yarda da wannan siffa da aka bawa Muawiyah ba.
Ya kara da cewa: “Daya daga cikin matsaloli da aibobii da ke tattare da silsilar ita ce, ba a siffanta ta da kyau, misali Mu’awiyah ya kasance mutum mai kiba mai yawan cin abinci, kuma Manzon Allah (SAW) ya la’ance shi da yi masa addu'ar rashin koshi, yayin da aka siffanta Mu’awiyah a matsayin mai kyakkyawan hali a fim ɗin. Misali, Musuluntar Muawiyah kafin a ci Makka wannan ba gaskiya ba ne. Wani abin da ya kunsa shi ne rashin bayar da labarin muhimman abubuwan da suka faru na tarihi, ta yadda za su ci gaba da kaiwa ga babbar manufarsu, wato tsarkake Muawiyah da Umayyawa.
Fuskar Muawiyah ta gaskiya tana boye a cikin fim ɗin
Masanin harkar fim Hujjatul Islam Adriani ya ce: "Wannan silsila tana neman tsarkake surar mutane irin su Abu Sufyan." Silsilar fim ɗin Muawiyah ta gabatar da Abu Sufyan a matsayin dan kallo a yakin Uhud, ba wai wanda ya tsaya gaba da gaba da Annabi Muhammad (SAW) ba.
Wannan masanin harkokin yada labarai ya bayyana cewa: Masu kallon wannan silsila sun shaida tsarkakewar Muawiyah; Kamar dai yadda Golani ya boye sunan ta'addancinsa a bayan karagar mulkinsa a Siriya, haka wannan silsila ta ke neman boye hakikanin Mu'awiyah.
.................................
Your Comment