Falasdinawa tare da dimbin yawansu na kasancewarsu a masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus da ake mamaya, sun zama wata garkuwa mai karfi daga mamaya da suka sanya wannan wuri mai tsarki a karkashin kawanya.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto daga shafin sadarwa na Shahab cewa, Fatima Khidr wata ‘yar gwagwarmayar Palasdinawa da ke zaune a birnin Kudus da aka mamaye, ta sanar da kara zafafa hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan take yi kan Falasdinawa a masallacin Al-Aqsa.
Ta ce: Mamaya sun hana masu ibada shiga masallacin Al-Aqsa, suna lakadawa mata da matasa duka da zaginsu, alhali suna barin sahyoniyawa 'yan kaka gida su gudanar da bukukuwan da ake kira "Talmud" a cikin masallacin Al-Aqsa, kuma hakan yana cikin inuwar goyon bayan da 'yan sandan haramtacciyar kasar Isra'ila suke ba wa matsugunan.
Ita dai wannan mata 'yar gwagwarmayar Palasdinu ta kara da cewa: Sojojin mamaya na birnin Kudus ne suka mamaye Masallacin Al-Aqsa; Ta yadda ya zama fagen fama. Kamara na lura da kowane motsi a cikin Masallacin Al-Aqsa da kewayensa. Hatta raba dabino da taimako ga masu azumi ‘yan mamaya sun hana su, kuma duk wanda ya shigo da abinci cikin masallacin Aqsa ana kama shi.
Khidr ta jaddada cewa: ‘Yan mamaya sun mayar da birnin Kudus wani sansanin soja. Domin tituna sun cika da jami'an 'yan sandan Isra'ila. Ana aikata munanan laifuka akan mazauna birnin Kudus. Bugu da kari, ana korar Falasdinawa masu fafutuka daga Masallacin Al-Aqsa da kuma birnin Kudus, na baya-bayan nan shi ne korar "Zinat Berber" saboda rike taswirar Falasdinu.
Ta ce: "Mazaunan Kudus suna jurewa duk da wannan mawuyacin yanayi". Wahalhalu da turjiya da mazauna zirin Gaza suka yi ya sanya mazauna birnin Kudus da ake mamaye da su kara tsayin daka da gwagwarmaya.
A gefe guda kuma Majid Abu Qutish babban jami'in kungiyar Hamas ya yi kira da a ci gaba da kasancewa a masallacin Al-Aqsa a sauran kwanaki na watan Ramadan, duk kuwa da haramcin da mamaya suka yi a wannan masallaci mai alfarma.
Ya kara da cewa: Manufofin 'yan mamaya da ayyukan soji da suke yi a birnin Kudus ba za su taba kawo cikas a yunkurin da Falasdinawa masu ibada suke yi na zuwa masallacin Al-Aqsa ba. Hotuna masu ban sha'awa na halartar masu ibada sun kasance wani sako na kalubale ga mamaya da kuma goyon bayan wurare masu tsarki da kuma kasar Falasdinu.
Wannan babban jigo na kungiyar Hamas ya jaddada cewa: Al'ummarmu masu daraja a Kudus, yankunan da aka mamaye, da kuma gabar yammacin kogin Jordan, kamata ya yi su kasance da faffadan kasancews da suke da shi a cikin masallacin Al-Aqsa, kuma hanawar mamaya da kawo cikas na soji kada ya hana su azama.
Abu Qutish ya ambaci Falasdinawa masu kare Masallacin Al-Aqsa a matsayin garkuwa mai karfi a cikin wannan masallacin da ke karkashin inuwar shirin ‘yan mamaya na yahudawa wannan wuri mai tsarki da kuma karuwar kwadayin sahyoniyawa mazauna kasar.
Bisa rahoton Kamfanin dillancin labaran iqna ya kawo cewa, tun daga watan azumin Ramadan mai alfarma, duk da tsauraran matakan da mamaya suka dauka a birnin Kudus da tsohon birninsa, dubban masallata ne ke gudanar da ibada a masallacin Al-Aqsa. A ranar Juma'a ta biyu na watan Ramadan, kimanin mutane 130,000 ne suka gudanar da sallah a masallacin Al-Aqsa, wanda hakan adadi mai yawa tun daga farawar watan Ramadan.
Your Comment