18 Maris 2025 - 05:14
Source: Irna
Shugabannin Hamas 5 Da Falasdinawa 412 Sukai Shahada A Harin Isra'ila Na Yau 

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa, ya zuwa yanzu mutane 412 ne suka yi shahada a hare-haren wuce gona da iri da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarto bisa nakaltowa daga shafin jaridar Yedioth Ahronoth a yau Talata cewa, bayan hare-haren da Isra'ila ta kai kan al'ummar zirin Gaza, baya ga shahada da raunata wasu fararen hula da kananan yara kimanin 700 a zirin Gaza, wasu manyan jami'an kungiyar Hamas biyar sun yi shahada ciki har da Ussam al-Dali mamba a ofishin siyasa na Hamas.

A cewar rahoton, Dr. Usam al-Dhaalis, ya fito daga sansanin Jabalia, kuma yana zaune a sansanin Nuseirat, ya kasance fitaccen shugaban kungiyar Hamas, kuma ya kasance shugaban kwamitin sa ido da bin diddigin gwamnati a zirin Gaza. A matsayinsa na daya daga cikin jiga-jigan kungiyar Hamas, ya taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da harkokin farar hula da ayyukan fararen hula a zirin Gaza. Al-Dhaalis ya kasance mai himma a cikin manufofin gwamnatin Hamas baki daya, sannan kuma ya kasance shugaban sashen malamai a Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA). Al-Daalis ya kuma taba zama tsohon mai ba Ismail Haniyya shawara.
Bahjat Abu Sultan, ɗaya ne daga shahidan a Gaza, ya kasance fitaccen jami'in Hamas, kuma shi ke da alhakin ayyukan cikin gida a Gaza. Ya rike muhimman mukamai da dama a ma'aikatar harkokin cikin gida da kuma jami'an tsaron gwamnatin Hamas a Gaza. Ya kuma halarci ziyarar gani da ido a Gaza, ciki har da ganawa tsakanin shugabannin Hamas da iyalan fursunoni.
Ahmed Umar Al-Khatti, wanda aka fi sani da Abu Umar, shi ma ɗaya ne daga shahidan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai wa Gaza hari da safiyar Talata. Ya yi aiki a matsayin Babban Darakta na Ma'aikatar Shari'a ta hukumar Hamas a zirin Gaza kuma ya yi suna a Gaza da karfafa tsarin shari'ar Musulunci a shekarar 2021, an zabe shi a matsayin shugaban kwalejin horar da 'yan sanda ta Rabat da ke Gaza.
Bisa labarin da Yedioth Aharonot ta fitar, babban jami'in kungiyar Hamas na hudu da ya yi shahada a safiyar yau shi ne Janar Mahmoud Abu Watfa, babban darektan ma'aikatar cikin gidan gwamnatin Hamas a Gaza. A cewar rahoton, shima ya yi shahada tare da iyalansa a wani harin da aka kai a gidansa da ke birnin Gaza. Bayan da tsagaita wutar ta fara aiki, a wata tattaunawa da ya yi da wani mazaunin Gaza, ya jaddada kudirin kungiyar Hamas na sake gina zirin Gaza, yana mai cewa: "Za mu sake gina Gaza da karfi fiye da da".
A cewar sanarwar da 'yan sandan Hamas suka fitar a watan jiya, Abu Watfa ya taka rawar gani wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar Gaza. Ta hanyar duba jami'an tsaro da 'yan sanda a zirin Gaza tare da jibge su a wurare daban-daban, ya jaddada rawar da 'yan sanda ke takawa wajen tabbatar da tsaron jama'a.
Shahidi Abu Ubaidah al-Jamasi wani jigo ne na kungiyar Hamas wanda ya taba rike mukamin shugaban kungiyar gudanarwa a kudancin zirin Gaza. A cewar rahoton Yedioth Ahronoth, bayyanarsa ta karshe a bainar jama'a ita ce a watan Yulin 2023, lokacin da ya halarci taron tunawa da Ramadan al-Saifi, daya daga cikin wadanda suka kafa kuma fitattun 'yan gwagwarmayar Hamas, kuma bai bayyana a bainar jama'a ba bayan haka.
A cikin watan Yulin 2017, Al-Jamasi ya zama shugaban sashin shari'a na Hamas, kuma a cikin wannan rawar ya yi kokarin cire wannan kungiyar daga cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda na Turai. Da ya nemi kotun da ta sake duba hukuncin da ta yanke, ya jaddada sahihancin gwagwarmaya kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.
A cewar majiyoyin Falasdinawa, an tabbatar da shahadar wadannan manyan jami'an Hamas biyar.
Abu Zuhri jami'in Hamas ya ce: Gwamnatin yahudawan sahyoniya na neman kafa yarjejeniyar mika wuya da jinin al'ummar Gaza ne
Sami Abu Zuhri ɗaya daga cikin shugabannin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya jaddada cewa laifukan da gwamnatin sahyoniyawa ke aikatawa a Gaza suna aiwatar da su ne da nufin rusa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma sanya yarjejeniyar mika wuya da suke son rubutata da jinin al'ummar Gaza.
Netanyahu zai kasa cimma burinsa kuma ya kamata ya sani cewa zaluncin nasa zai sanya hannu kan sammacin kisa ga fursunonin sahyoniyawan.
Domin Fursunoni 3 na Isra'ila sun mutu tare da jikkata sakamakon wani kazamin harin bam da aka kai a zirin Gaza
Wani shugaban kungiyar Hamas ya sanar da kashees tare da raunata wasu fursunonin Isra'ila a zirin Gaza.
A cewar rahoton, wani fursinoni Isra'ila ya mutu, yayin da wasu fursunoni biyu suka jikkata, a wani kazamin harin da sojojin Isra'ila suka kai a zirin Gaza.
Jami'in Falasdinawa ya ce babban burin Netanyahu shi ne kawar da fursunonin Isra'ila.

Your Comment

You are replying to: .
captcha