Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a yammacin yau Lahadi.
Dangane da harin da Amurka ta kai, mun kai hari kan jirgin Amurka USS Harry Truman da makami mai linzami 18 na ballistic da na cruise da kuma jirgi maras matuki.
Ya kara da cewa domin mayar da martani ga hare-haren da aka kai wa kasarmu, ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen kai wa dukkan jiragen yakin Amurka hari a tekun Bahar Maliya da Tekun Larabawa.
Makiya Amurka sun kai hari a Sanaa babban birnin kasar da larduna 7 tare da kai hare-hare sama da 47 a kasarmu.
Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya sanar da cewa, a cikin 'yan sa'o'i da suka gabata ne Amurka ta kai hare-hare ta sama sama da 47 a kan yankunan kasar Yemen.
Saree ya bayyana cewa, wadannan hare-haren sun shafi yankuna daban-daban a lardunan Sana'a, Saada, Al-Bayda, Hajjah, Dhamar, Marib, da Al-Jawf, inda ya kara da cewa: Mutane da dama ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon wadannan hare-haren na Amurka.
Your Comment