Ma'aikatar lafiya ta Yemen ta sanar da cewa, fararen hula 132 ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Amurka ta kai kan fararen hula a Sanaa da lardunan Saada da Bayda. Bisa kididdigar farko, an kashe fararen hula 31, yayin da wasu 101 suka jikkata a wadannan hare-haren, wadanda akasarinsu mata ne da kananan yara.
A safiyar yau Lahadin, Amurka da Birtaniya sun kai hare-hare kan wasu unguwanni da wuraren zama a biranen Sanaa, Saada, Dhamar, Marib, da Taiz, da jiragen saman yakin Amurka da na Birtaniya, tare da harin makami mai linzami da jiragen yakin Amurka suka kai a tekun Bahar Rum.
Ma'aikatar, yayin da take yin Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai kan fararen hula da wuraren zama a Yemen, ta jaddada cewa: "Wannan babban laifin yaki ne da kuma keta dokokin kasa da kasa".
Wasu yankunan kasar Yemen da suka hada da birnin Sanaa da Sa'ada sun fuskanci hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Birtaniya suka kai a safiyar yau Lahadi.
A baya ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya sanar a cikin wata sanarwa cewa: Hare-haren da Amurka da Birtaniyya suka kai kan wasu unguwanni a birnin Sana'a aiki ne na yaki da aikata laifukan ta'addanci.
Sanarwar ta kara da cewa: Kai hari kan fararen hula da matsugunan jama'a, babban laifin yaki ne, kuma wata alama ce ta ta'addancin Amurka ga kasashe da al'umma da ta ke adawa da su.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: Wannan zaluncin ya sake nuna cewa Amurka na yaki ne a madadin gwamnatin Sahayoniya.
Ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah ta Yaman ya kara da cewa wuce gona da iri ba zai iya hana kasar Yamen taimakon al'ummar Palastinu da kuma sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na tallafawa zirin Gaza ba.
A karshe sanarwar da aka fitar ta nanata cewa: Wannan ta'asar ba za ta tafi ba tare da an mayar da martani ba, kuma dakarun kasar Yemen sun shirya tsaf domin tunkarar wadannan munanan hare-haren".
Your Comment