17 Faburairu 2026 - 22:42
Source: ABNA24
Jagoran Juyin Juya Halin: Makamin Nutsar da Jirgin Yakin Ya Fi Hadari Fiye da Jirgin Yakin

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Imam Sayyid Ali Khamenei, ya yi ishara dangane da  barazanar da Amurka ke ci gaba da yi na tura jiragen yakin zuwa Iran, yana mai jaddada cewa "jirgin yaki yanki ne mai hatsari na yaki, amma makaman da ke iya nutsar da shi zuwa kasa na teku sun fi shi hatsari."

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: A safiyar yau, Talata, yayin wani taron ganawa da yayi da wasu gungu na mazauna lardin Gabashin Azerbaijan, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Imam Khamenei, ya ce: "Da alama shugaban Amurka ya dage kan maimaita ikirarin cewa sojojinsu su ne mafi karfi a duniya. Amma zai iya yiwuwa rundunar da ta fi karfi a duniya wani lokacin ta iya fuskantar mummunan shan kayen da har ba za su iya murmurewa ba. Kullum yana cewa, 'Mun aika jiragen ruwanmu zuwa Iran.' To, jirgin ruwan yaki babu shakka kayan aiki ne mai hatsari, amma makaman da ya fi hatsari shi ne wanda zai iya nutsar da wannan jirgin ruwan zuwa kasan teku".

Jagoran ya ƙara da cewa: "Shugaban Amurka ya ambata a cikin ɗaya daga cikin maganganunsa na baya-bayan nan cewa Amurka ba ta iya kawar da Jamhuriyar Musulunci ba na tsawon shekaru 47; yana mai yin korafi game da wannan ga al’ummarsa". Tsawon shekaru 47, Amurka ba ta iya kawar da Jamhuriyar Musulunci ba; wannan kyakkyawan Ikrari ne. Kuma ina gaya masa: Kai ma ba za ka iya yin hakan ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ƙara da cewa: Waɗannan su ne kalmomin da shugaban Amurka ya faɗa; wani lokacin yana barazana, a wasu lokutan yana ba da umarni game da abin da ya kamata a yi da abin da bai kamata a yi ba. Wannan yana nufin suna neman mamaye al'ummar Iran ne.

Jagoran ya jaddada cewa al'ummar Iran, tare da al'adunsu, tarihinsu, da kuma babban matakin ilimi, ba za su yi mubaya'a ga shugabanni kamar waɗannan mutane lalatattu ba waɗanda ke riƙe da madafun iko a Amurka a yau ba.

Ya ci gaba da cewa: Suna cewa: Bari mu yi tattaunawa kan makamashin nukiliyarku, kuma sakamakon tattaunawar zai zama hana ku anfani da su. Idan tattaunawa ta zama dole, to babu wani amfani a cikinta, kuma idan dole ne a gudanar da ita, to yanke hukunci kan sakamakonta tun ba’a je ko ina ba kuskurene kuma wauta ne. Kuna cewa: Bari mu yi magana game batu kaza da kaza, mu kuma cimma matsaya. Me ya sa kuke ƙaddara sakamakon? Dole ne mu cimma wannan yarjejeniya! Wannan wauta ce. Wannan shi ne abin da shugabannin Amurka da wasu sanatoci da shugaban ƙasa na yanzu, da sauransu suke yi.

Jagoran juyin juya halin ya ƙara da cewa: Jamhuriyar Musulunci tana nufin Al’umma rayayya. Jamhuriyar Musulunci ba gwamnati ba ce da taai hannun riga da al’umma ba. Jamhuriyar Musulunci ita ce al'ummar Iran din - wannan ƙasa mai juriya, mai ƙarfi, al'umma da ta shirya yin aiki tuƙuru da kuma ƙoƙarin ci gabanta. Kuma, godiya ta tabbata ga Allah, ta ci gaba a cikin waɗannan shekaru arba'in da bakwai da suka gabata.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba: A wancan lokacin, lokacin da Jamhuriyar Musulunci take ƙaramar shuka, bai yiwu an iya tuɓeke ta ba. A yau, Alhamdulillah, Jamhuriyar Musulunci ta zamo bishiya mai tsayi da kafuwa, mai ‘ya’ya mai albarka.

A wani ɓangaren kuma, Jagoran juyin juya halin ya jaddada cewa dole ne jami'ai su ninka ƙoƙarinsu, yana mai nuna cewa hauhawar farashin kaya da rugujewar kuɗin ƙasa ba su da ma'ana.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi magana game da tawayen da aka yi a watan Disamba da ya gabata da kuma shahidai da wadanda abin ya shafa, yana mai cewa: " Tabbas an zubar da Jini a kasa. Muna cikin makoki. Ina cewa muna makokin jinin da aka zubar. Wasu daga cikinsu su na daga cikin lalatattu masu tunzurawa akan fitinar, da kuma wadanda suka shirya juyin mulkin kansu, wasu kuma wadanda ba a ba su isasshen lokaci ba sun dawo cikin hayyacinsu, kuma hukuncinsu yana tare da Allah. Ba mu da wata alaka da su. Amma akwai wasu da ba sa cikinsu. Akwai rukuni uku, gungu uku ne. Ina raba matattu da wadanda abin ya shafa zuwa rukuni uku. Akwai rukuni na rundunonin da ke kare tsaro da kuma kiyaye tsari, sun kasance jami'an tsaro ne ko sojojin Basij ko masu tsaron juyin juya hali, ko wadanda suka yi aiki tare da su; sun yi shahada. Waɗannan suna cikin mafi kyawun shahidai. Wannan rukuni ne daya daga cikinsu".

Ya ci gaba da cewa: “Akwai gungu na masu wucewa da bain ya rutsa da su; idan wani mai tayar da zaune tsaye ya tayar da zaune tsaye a cikin birnin, sai waɗanda suka tunkare shi kawai ake kashewa, mutane marasa laifi suna tafiya a kan titi suna tafiya zuwa aiki da gidajensu; da yawa daga cikinsu sun yi shahada. Waɗannan ma, shahidai ne saboda sun yi shahada a cikin tawayen abokan gaba. Duk inda wannan Harsashin ya fit to wannan lamari yana faru ne a tsakanin fitinar abokan gaba, kuma waɗannan da aka kashe suma shahidai ne. Rukunin na biyu suma shahidai ne.

Imam ya ci gaba da cewa: Rukunin na uku su ne waɗanda aka yaudare su, suka yi aiki ba tare da wayo ba, ba su da ƙwarewa, kuma suka shiga cikin masu tayar da zaune tsaye. Ina so in ce sun fito daga cikinmu, su ma 'ya'yanmu ne, kuma wasu daga cikinsu sun tuba. Wasu daga cikinsu sun rubuta mini suna cewa, "Mun fita ne kan titi a wannan rana kawai," da sauransu. Ku yafe mana. Ba sa cikin kurkuku; sun 'yantu, amma sun yarda da kuskurensu. Sun tuba. Sun yi kuskure. Waɗanda aka kashe daga cikinsu hukumomi sun ɗauke su a matsayin shahidai, kuma sun yi kyautata wajen yin hakan. Ya ci gaba da cewa: Saboda haka, da'irar shahidainmu waɗanda muke ɗaukar su a matsayin shahidai abu ne mai faɗi. Banda waɗanda suka tayar da fitina da shugabanninsu, da waɗanda suka karɓi kuɗi daga abokan gaba suka ɗauki makamai, ban da su, sauran - ko jami'an tsaro ne ko masu wucewa ko ma waɗanda suka yi tafiya kaɗan tare da masu tayar da fitina - waɗannan 'ya'yanmu ne; muna neman rahama da gafara a gare su. Sun yi kuskure. Muna roƙon Allah Maɗaukaki Ya gafarta musu kuskurensu, In sha’a Allah.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha