12 Maris 2025 - 10:01
Source: ABNA24
Kungiyar Hamas Ta Yi Gargadi Kan Laifukan Da Hukumar Falasdinawan Ta Ke Aikatawa

Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta yi gargadi game da ci gaba da aikata laifukan da jami'an tsaro na PA ke yi.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: a safiyar yau Talata kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Palasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa: Ci gaba da kai hare-hare kan al'ummar mu da kuma gwagwarmaya da jami'an tsaron gwamnatin Palasdinu ke yi wani lamari ne mai hadari da ke nuna dagewarsu wajen zubar da jinin Falasdinawa. ƙungiyar a cikin wata sanarwa ta ce: "Mummunan laifin da ya kai ga shahadar Abdul Rahman Abu Meni ta hanyar harbin bindiga da jami'an tsaro na PA suka yi ya nuna irin yadda suka sha'awar zubar da jini". Kamfanin dillancin labaran Aljazeera ya kawo cewa: Muna jimamin shahadar Abu Mina tare da yin gargadi kan mummunan ta'addacin da hukumomin Falasdinawan ke ci gaba da aikatawa. “Muna kira ga dukkan bangarorin da ke yankin Yammacin Kogin Jordan da su sa baki cikin gaggawa don hana zubar da jini daga jami’an tsaron gwamnatin.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha