Rushewar gwamnatin yahudawan sahyoniya da kara nuna damuwa game da rugujewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza
A yayin da kashi na farko na shirin tsagaita wuta da musayar fursunoni tsakanin gwamnatin sahyoniya da kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas ya kawo karshe, majalisar ministocin Netanyahu ta nuna damuwarta game da sake dawo da yakin da ake yi da zirin Gaza, ta hanyar kawo cikas ga tattaunawar da ake yi na aiwatar da kashi na biyu na tsagaita bude wuta.
A ranar 19 ga watan Janairu ne aka fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza, tsawon zangon farko na yarjejeniyar ya kasance kwanaki 42 bayan kawo karshen wannan lokaci, gwamnatin yahudawan sahyuniya na kawo cikas tare da kawo tsaiko ga yunkurin aiwatar da kashi na biyu na yarjejeniyar. Tashar Talabijin ta 12 ta gwamnatin Sahayoniyya ta yi ikirarin cewa tawagar gwamnatin sahyoniyawan da ke tattaunawa a birnin Alkahira za ta koma Tel Aviv sakamakon adawar da Hamas ta yi na tsawaita zangon farko na tsagaita wuta. Hamas dai na son gudanar da wani mataki na biyu na shawarwarin tsagaita wuta da zai kawo karshen yakin, yayin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ke son tsawaita kashi na farko na tsagaita wutar.
Ba wai kawai Amurka ta fito fili tana goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan ba wajen neman tsawaita zangon farko na tsagaita bude wuta, sai dai harma ta gabatar da wani shiri kan wannan batu. Ofishin firaministan gwamnatin Sahayoniya ya sanar da safiyar Lahadi cewa, bayan shawarwarin tsaro da Benjamin Netanyahu ya jagoranta, an yanke shawarar cewa Isra'ila za ta amince da shirin dan aiken musamman na Trump kan yankin gabas ta tsakiya, Steve Wittkoff, na tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza a cikin watan Ramadan da kuma bukukuwan Idin Ƙetarewa.
Shawarar da wakilin Trump ya gabatar ba su yi dubi ga ko wace hanya ban a tsokaci kan manyan sharuddan da ‘yan gwagwarmaya suka gindaya na sakin sauran ‘yan sahayoniyawan da suka yi garkuwa da su a zirin Gaza, kamar dakatar da yakin gaba daya, da janyewar daukacin sojojin gwamnatin sahyoniyawan daga Gaza, da kuma farkon shirin sake gina yankin. Don haka shirin da kuma tsawaita kashi na farko na tsagaita bude wuta ya fuskanci adawa daga kungiyar Hamas. Dangane da haka Mahmoud Mardawi daya daga cikin jagororin kungiyar Hamas ya ce: "Ba za mu taba amincewa da tsawaita kashi na farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba, kuma bisa abin da aka rattabawa hannu, muna son a aiwatar da dukkan bangarorin yarjejeniyar".
Wadannan kura-kurai da rugujewar hadin gwiwa na Amurka da gwamnatin yahudawan sahyoniya sun sa gwamnatin sahyoniyawan ta hana shigar da kayayyaki da kayan agaji zuwa Gaza domin matsawa Hamas lamba. Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, gidan radiyo da talabijin na Isra'ila ya bayar da rahoton cewa, majalisar ministocin gwamnatin kasar ta umurci sojojin da su rufe duk wata hanya da ke kai wa zuwa zirin Gaza. Rahoton ya ce Benjamin Netanyahu, firaministan gwamnatin Sahayoniya, tare da hadin gwiwar Amurkawa ne suka dauki matakin.
Dangane da matakin da Netanyahu ya dauka na hana shigar da kayayyaki da kayan agaji a zirin Gaza, ofishin yada labarai na gwamnatin Falasdinu a zirin Gaza ya bayyana cewa: Hana shigowa da kayan agajin cikin zirin Gaza yana nufin kakaba yunwa ga mazauna wannan yanki, wadanda suka dogara kai tsaye kan wannan taimako. Mahmoud Mardawi ya kuma jaddada cewa ana yaudarar Netanyahu da cewa zai iya rama cin kashin da ya sha a kasa ta hanyar kashe 'yan kasar kuma zai iya cimma burinsa ta haka, amma ba za a taba matsa mana ba kuma ba za mu amince da wannan shiri ba. Idan aka yi la’akari da yanayin da ya kunno kai, damuwa kan gazawar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da sake barkewar yakin da majalisar ministocin gwamnatin Sahayoniya ta yi ya rubanya.
Your Comment