4 Maris 2025 - 22:34
Yawan Shahidan Gaza Ya Karu Zuwa 48,405

A yayin da aka tono gawarwakin wasu shahidai da dama daga karkashin baraguzan gine-gine a yankuna daban-daban na Gaza, adadin shahidan da gwamnatin mamaya ta haifar a wannan yakin tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ya karu zuwa shahidai 48,405.

Kamfanin dillancin labaran Abna ya habarta maku bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na IRNA cewa, ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta fitar da wata sanarwa inda ta sanar da cewa a cikin sa’o’i 24 da suka gabata an ciro gawarwakin shahidai 7 daga karkashin baraguzan gine-gine sannan kuma wani Bafalasdine daya ya yi shahada sakamakon raunukan da ya samu a harin da ‘yan mamaya suka kai a zirin Gaza.

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta kara da cewa: Haka kuma, an kai mutane 11 da suka jikkata zuwa asibiti a daidai wannan lokacin.

A cewar wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta fitar, adadin shahidai a yankin ya karu zuwa shahidai 48,405 tun daga farkon hare-haren wuce gona da irin na gwamnatin mamaya a ranar 7 ga Oktoban 2023.

Ma'aikatar ta kuma sanar da cewa adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa 111,835.

A cewar IRNA, sojojin Isra'ila sun gaza cimma manufofin da suka ayyana a tsawon kwanaki 471 na yaki da kisa a zirin Gaza, inda a karshe aka tilasta musu amincewa da shan kaye a tinkarar gwagwarmaya da kuma yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

A karshe bayan da aka yi ta cece-kuce da takun saka na cikin gida tsakanin yahudawan sahyoniya da ministocin gwamnatin kasar, yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza ta fara aiki a yammacin Lahadi 20 ga watan Janairu.

An tsara aiwatar da wannan yarjejeniya tare da kammala shi a matakai uku, amma kawo yanzu ba ta shiga mataki na biyu ba saboda cikas da gwamnatin Isra'ila ta yi.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha