Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) – ABNA – ya habarta maku cewa: An yi jana’izar gawarwakin mayakan Hizbullah 3 da suka yi shahada a kasar Lebanon, wadanda ke da suna kamar haka: "Rami Nazi Zainuddin" da ake yi wa lakabi da "Abu Hasan", "Muhammad Shauqi Salamah" da ake yi wa lakabi da "Abu Turab" da "Adham Fawzi Zainuddin” da ake yi wa lakabi da "Abu Ali" an binne su a garin "Al-Jumaijama" da ke kudancin kasar nan tare da halartar mutane daban-daban.