23 Oktoba 2024 - 08:13
Samun Nutsuwa A Fagen Fama; Maimaita Irin Shahadar Sinwar, A Wannan Karon Tare Da Shahadantar Da Wani Mayakin Hizbullah + Bidiyo

Bidiyon fafatawar da mayakan Hizbullah na kasar Labanon ke yi da sojojin yahudawan sahyoniya ya zama batun wasu shafukan sadarwa na zamani, wanda a cewar masu amfani da shi, yana tunatar da mu irin jarumtar Yahya Sinwar.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta cewa: gwamnatin yahudawan sahyoniya ta fitar da wani faifan bidiyo na wani mayakin kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon a yankin arewacin kasar da ta mamaye inda shi akdai yake fafatawa da cikin nutsuwa Sojojin Isra'ila a daya daga cikin kauyukan kan iyaka.

Natsuwarsa mai ban mamaki da wannan mayaka na Hizbullah ya samu a yayin harba makaminsa, tare da saninsa akan irin ayyukan leken asiri ta sama da kuma yawan bama-baman da aka jefawa a kauyukan da ke kan iyaka da Labanon, ya sanya jama'a da dama sun yaba masa kuma ya zama abin alfahari da daukaka a gare su.

Kamar yadda ya bayyana a karshen fim din, kawai gwamnatin sahyoniyawan ta jefa bam mai tarin yawa tare da tarwatsa gidaje da dama domin ta kasha mayakin Hizbullah guda daya kacal. Tabbas, kuma ba a bayyana ko wannan mayakin ya iya sauya wajen da yake  kafin kai harin ta sama ba ko a'a.



A cewar wasu majiyoyin yada labaran kasar Labanon, jarumin da ke cikin fim din ana kiransa da suna "Ibrahim Haider" wanda ya samu falalar shahada. Wasu dai na ganin irin jaruntakar da wannan dan gwagwarmayar Hizbullah ya nuna a yakin da dakarun yahudawan sahyoniya suke yi, wani lamari ne da ke tuno da jarumtar Yahya Sinwar Mujahid Palastinu kuma babban sakataren kungiyar Hamas, wanda ya zama wata alama ta jajircewar dakarun gwagwarmaya a kan sojojin yahudawan sahyoniya a duniya.

An kuma buga faifan bidiyo na wannan shahidi na gwagwarmaya, yana mai cewa: Shugabanmu shi ne Sayyidina Sahibaz-Zaman kuma dukkan mu za mu yi yaki a cikin sojojinsa. Ko da mun yi shahada za mu komo tare da shi. Zai bayyana tare da rundunar shahidai har sai mun samu adalci da taimakon wadanda aka zalunta.

و سیعلم الذین ظلموا ای منقلب ینقلبون والعاقبه للمتقین.