A tsawon fiye da shekara guda na
yakin Gaza gwamnatin sahyoniyawan ta kashe daukacin iyalan Palastinawa 1206
tare da goge sunayensu daga shafin tarihi.
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa gwamnatin sahyoniyawan ta kawar da dukkanin iyalan Falasdinawa 1206 tun bayan da aka fara yakin kisan kare dangi a zirin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
A cewar sanarwar da ma'aikatar lafiya ta Gaza ta fitar, adadin iyalai a zirin Gaza inda dukkanin 'yan dangin suka yi shahada in banda mutum daya ya kai 2271.
Wannan kungiyar Falasdinu ta bayyana cewa: Haka kuma, adadin iyalan da aka yi wa kisan kare dangi da fiye da daya daga cikin mambobinta da suka tsira ya kai iyalai 3110.
Bisa kididdigar baya-bayan nan; Palasdinawa dubu 42 da 438 ne suka yi shahada a hare-haren sahyoniyawan sannan kuma mutane dubu 99 da 246 suka jikkata, mafi yawansu mata da kananan yara.