17 Oktoba 2024 - 19:54
A Hukumance Gwamnatin Sahyoniya Ta Yi Iƙirarin Kashe Yahya Sinwar

Yahya Sinwar: Ba ma tsoron a kashe mu a tafarkin kare addininmu da kasarmu da wurare masu tsarki, kuma jininmu da rayuwarmu ba su fi na dan karamin shahidi Palastinu daraja ba.

Ministan harkokin wajen yahudawan sahyoniya a wani sako da ya aikewa takwarorinsa na duniya ya yi ikirarin cewa wannan gwamnatin ta kashe Yahya Sanwar shugaban Hamas.

Wannan dai shi ne karo na hudu da gwamnatin yahudawan sahyoniya ke yin ikirarin kashe Yahya al-Sanwar.

Ministan yakin gwamnatin sahyoniyawan da ke kan iyakar Gaza ya yi ikirarin cewa: Mun rufe shari'ar fayil ɗin Sanwar.

A wani taron manema labarai da ministan yakin gwamnatin sahyoniyawan Yoav Gallant ya yi daga kan iyakar Gaza, a hukumance ya yi ikirarin shahadantar da Yahya Sinwar, ya kuma ce yana godiya ga bangarorin sojoji da na Shabak da suka kai wannan harin na kisan gilla.

Gallant ya yi da'awar cewa kisan Sinwar sako ne ga iyalan fursunonin Isra'ila cewa wannan gwamnati za ta yi duk abin da zai yi sanadiyar dawo da wadannan fursunoni!

Shima Netanyahu yayi da'awar cewa: Sojojin mu ne suka kashe Sinwar.

Firaministan yahudawan sahyoniya ya bayyana a wani faifan bidiyo cewa sabon shugaban kungiyar Hamas ba ya raye kuma sojojin wannan gwamnatin sun kashe shi.

Ya yi ikirarin cewa za mu yi amfani da dukkan kokarinmu wajen dawo da fursunoninmu.