13 Oktoba 2024 - 06:31
Hukumar Bahrain Ta Kama Allamah Al-Sadady

Jami'an tsaron gwamnatin Al-Khalifa sun kama Allah Shekh Sudady saboda yayi kira da a karfafi Al’ummar Falasdinu da Da Lubnan

A jiya ne jami'an tsaron gwamnatin Al-Khalifa suka gayyaci Sheikh Ali al-Sadadi, kuma har yanzu yana tsare saboda yyai bayani kan guguwar Al-Aqsa da kuma yabawa kungiyar gwagwarmaya ta Lubnan bias goyon bayansu ga Gaza Falasdinu ta hanyar sadaukarwar da wannan suke ta yi.

Bayan shahadar Sayyid Hasan Nasrallah jami'an tsaron gwamnatin Al Khalifa sun kame mutane da dama a yankuna daban-daban na kasar Bahrain saboda yin Allah wadai da wannan ta'addanci.