Shugaban kasar Venezuela a
matsayin mayar da martani ga shahadar Sayyid Hasan Nasrallah a cikin wata
sanarwa da ya fitar ya yi kakkausar suka ga laifukan da gwamnatin haramtacciyar
kasar Isra'ila ta aikata inda ya ce: Al'ummar Palastinu da Labanon suna
fuskantar kisan kare dangi da ayyukan ta'addanci na gwamnatin Netanyahu mai
kisa. Laifukan da ya aikata suna tuna da kama ayyukan Hitler.
Shugaba Maduro ya tabbatar da cewa: “An bayar da umarnin wannan harin ne daga hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York. Matsorata na duniya sun yi shiru, amma ba wanda zai iya rufe bakin mutanen da yunkura”.