Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya habarta
cewa: Ayatullah Safayi Bushehri, wakilin jagora a lardin Bushehr a
safiyar yau a wajen faretin da sojojin kasar suka yi bisa zagayowar ranar farko
ta makon tsaro mai alfarma ya bayyana cewa: Daya daga cikin muhimman abubuwan
da wata kasa ya yakamata tana da shi shi ne ce ikon karfinta na rundunonin soji
a duk fannoni na tsaro.
Ya kara da cewa: A duk lokacin da wata kasa ke da wannan bangaren na karfi to kuma take da matsayi na musamman a tsarin tsaro da na'urorin tsaro na duniya, to zai zamo kasar tana da ikon kasa da kasa.
Ayatullah Safayi Bushehri ya jaddada cewa: Ko a halin yanzu sojojin Jamhuriyar Musulunci suna da iko mai girma da yawa na soji a dukkan bangarori na lissafin bangaren karfin tsaro.