19 Satumba 2024 - 19:26
An Gudanar Da Gasar Faretin Girmamawa Ga Manzon Allah (S.A.W.W) A Abuja + Hotuna

Yankin Imam Husain (a.s) wato Kano da kewaye sukai na ɗaya.

A cigaba da taron makon haɗin kai da ake yi lokacin bukukuwan Mauludin Manzon Allah (s.a.w.w) da harkar musulunci ƙarƙashin Jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ta saba gabatar duk shekara a yau Alhamis 16 ga watan Rabi'ul Auwal an Shiga rana ta biyar, bayan kammala Musabakar Alqur'ani mai girma tsakanin ɗaliban Fudiyyoyi, an gudanar da gasar Faretin girmamawa ga Manzon Allah (s.a.w.w), Inda Makarantun Fudiyya daga sassa daban daban na jihohin Najeriya suka kara a tsakanin su, daga bisani yankin Imam Husain (a.s) wato Kano da kewaye sukai na ɗaya, Sannan yankin Rasulul Akram Wanda ya haɗa Bauchi, Gombe da Darazo sukai na biyu.

- Abuja Struggle Reporters