Wannan shine matanin rubutun da aka fitar daga ofishin babban malamin kuma shugaban harkar musulunci a Nigeria Sheikh Ibrahim Ya'aqub Alzakzaky Hf
بسم الله الرحمن الرحیم
Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai
إنا لله وإنا إليه راجعون
Sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ke aukuwa a Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyar rashin rayuka da jikkata jama'a masu yawa, tare da hasarar dukiyoyi da dama, Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na jajanta ma iyalan dukkan waɗanda wannan bala'i ya shafa. Ya yi kira ga hukumomi da su ɗauki duk matakan da suka dace don gyara barnar da aka samu.
Jagora (H) ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya kuma gaggauta samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.
08/RabiuAwwal/1446
11/09/2024
Ambaliyar Ruwan Borno
@Szakzakyoffice












