Kamar yadda shafin labarai na Imn,
Sayyidina Hasan bin Ali bin Muhammad (AS) wanda aka fi sani da Imam Hasan
Askari (AS) dan Imam Hadi (AS) ne, kuma mahaifin Imam Mahdi (AS) wanda a ke shi
ne Imami kuma shugaban Shi’a na goma sha daya. Bayan shahadar mahaifinsa ya
karbi Imamanci yana dan shekara 22 kuma ya kasance Imamin Shi'a na tsawon
shekaru 6. Imamancinsa ya kasance karkashin kulawa da sa idon gwamnatin lokacin
a lokacin khalifancin Abbasiyawa. Daga karshe Imam Hasan Askari (AS) an shayar
dan shi guba bisa umarnin Mu’atamid Abbasi kuma ya yi shahada a ranar 8 ga
watan Rabi’ul Awwal shekara ta 260 kuma an binne shi a garin Samarra kusa da
kabarin mahaifinsa.
Ranar Shahadar Imam Hasan Askari (AS) Bisa Kalandojin Uku Na Duniya
Ranar shahadar Imam Hassan Askari (AS) a kalandar Shamsi ta kasance ranar Alhamis 22 Shahrivar 1403.Tabbataccen lokacin shahadar Imam Hasan Askari (AS) a kalandar Qamariya ita ce 8 Rabi’ul-Awl 1446. Takaitaccen lokacin shahadar Imam Hasan Askari (AS) a kalandar Miladiyya ita ce 12 ga Satumba, 2024.
Tarihin Imam Hasan Askari (AS)
An haifi Imam Hasan Askari (AS) a shekara ta 232 bayan hijira (847 Miladiyya) a garin Madina Munawwara. Imam Hasan Askari (amincin Allah ya tabbata a gare shi) dan Imam Ali An-Naqi (a.s.) ne, kuma mahaifin Imam Mahdi (a.s) Imami kuma shugaban Shi'a na sha daya. Mahaifiyarsa wata salihar mace ce mai tsoton Allah sunanta "Hadithah" (a.s), wadda wasu suka ce da ita "Susan".
Sunansa Da Alkunyarsa Da Lakubbansa:
Sunansa Hasan kuma ana masa alkunya da sunan Abu Muhammad. A wasu littafan kuma an ambaci wasu Alkunyoyinsa kamar: Abul Hajah, Abul Hasan da Abul Qaim. Laƙubbansa: Mafi shaharar laƙabin Imam shine "Askari". Ana kiransa da sunan “Askari” ne domin Imaminmu na 11 an tilasta masa zama a unguwar “Askar” a cikin “Samarra” bisa umarnin halifan Abbasiyawa. Daga cikin mashahuran laƙabin wannan Imamin ana iya ambaton "Naqi", "Zaki", "Fadill", "Amin".
Matansa Da Yaransa:
Dangane da sunan matar Imam Hassan Askari (AS). An ambaci sunaye da dama kamar Narjis, Raihan, Susan, Suqail da Maryam a cikin littafan tarihi. kuma babu cikakken bayani kan wannan batu. Watakila daya daga cikin dalilan shi ne boye haihuwar Imam Mahdi (A.S.). A cikin labarin da ya shahara a wurin mutane, an ce Sayyidah Narjis Khatun diyar sarkin Daular Rumawa ta Gabas ce, matar Imami na 11 kuma mahaifiyar Mahdin Alkawari (AS).
Shi’a sun yi imani da cewa Imam Hasan Askari (a.s.) ba ya da wasu ‘ya’ya, sai Imam Mahadi (a.s.) da aka yi alkawarin zuwansa wand a zai mulki kasa ya cika ta da adalci kamar aydda aka cika ta da zalunci. Shaikh Mufid ya rubuta a cikin littafin Al-Irshad cewa: “Hasan bin Ali Askari (A.S.) bai bar wasu ‘ya’ya ba sai Sahibaz-Zaman.
Tsawon Zamanin Imamancin Imam Hasan Askari (AS)
Imam Hasan Askari (AS) ya kama Imamanci ne a shekara ta 254 bayan hijira, bayan shahadar mahaifinsa mai daraja, kamar yadda yazo a wasiyya da hadisan Imam Hadi (AS) kan Imamancinsa ya ci gaba har tsawon shekaru shida.
Shahadar Imam Hasan Askari (AS)
Imam Hasan Askari (AS) ya yi shahada ne a ranar 8 Rabi’ul Awl shekara ta 260 bayan hijira a birnin Samarra bisa umarnin Khalifan daular Abbasawa Mutamid, ta hanyar sanya masa guba.
Inda Aka Binne Imam Hasan Askari (AS).
An binne wannan limami mai daraja a kusa da hubbaren mahaifinsa da ke Samarra. Bayan wani lokaci, an gina wurin ziyara a wannan wuri da ake kira da Askarain daya daga cikin wuraren ziyar Shi'a a kasar Iraki.
Gabatar Da Nada Imam Mahdi (AS) Ga 'Yan Shi'a
Daya daga cikin muhimman ayyukan Imam Hasan Askari (AS) shi ne gabatar da dansa ga al'ummar Shi'a. Wannan al’amari yana da muhimmanci, domin kuwa a daya bangaren makiya Imam Zaman (A.S) suna kokarin nemansa su shahadantar da shi. Domin a hadisai da dama yazo cewa sun san cewa za a haifi yaro daga gidan Ahlul Baiti (A.S) wanda zai kasance mai ceton duniya kuma mai turmuza azzalumai kuma ba zai yi mubaya'a ga azzalumai ba kamar yadda iyayansa da kakanninsa ba su yi ba. Don haka suka dauki matakai da dama don hana haihuwar Imam, har ma suka yi shirin kashe Imam Hasan Askari (a.s.). Kamar yadda ya zo a cikin hadisai, an kwatanta haihuwar Imam Zaman (AS) da haihuwar Annabi Musa (AS).
Imam Askari (AS) ya zama wajibi ya gabatar da dansa ga gungun dattawan Shi’a da amintattun mutane. Sun kuma isar da labarin haihuwarsa ga sauran mabiya Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, ta yadda a yayin gabatar da wannan ma'abocin girma, ba za a samu wata barazana ga jakadan gaskiya na karshe ba. Muhammad bin Uthman da wasu dattijon ‘yan Shi’a sun ruwaito cewa: Mun tara ‘yan Shi’a arba’in a gaban Imami na 11. Ya nuna mana dansa ya ce: "Bayana, wannan shi ne limaminku kuma magajina." Ku karɓi umarni daga gare shi, kada ku rarraba a cikin addininku a bayana, domin za ku halaka kuma ba za ku ƙara ganinsa ba daga yau".
Imamancin Imam Mahdi (AS)
Ranar 9 ga watan Rabi’ul Awwal, kwana daya da shahadar Imam Hasan Askari (AS), ita ce ranar da ‘yan Shi’a ke murnar fara Wilaya da Imamancin Imam Mahdi (AS), kuma wasu daga cikinsu suna neman biyan bukatarsu ta hanyar tawassuli ga Imaminsu.