Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku cewa: a yau asabar Ali Shamkhani ya rubuta a cikin kafar
sada zumunta cewa: Burin gwamnatin sahyoniyawa na kashe masallata a makarantar
Tabiin a Gaza tare da kashe shahid Isma'il Haniyyah a kasar Iran shi ne neman
yaki da kuma karya tattaunawar tsagaita wuta.
Ya kara da cewa: "Tsarin doka, diflomasiyya da kafofin watsa labarai da aka gudanar sun shirya shirye-shiryen hukunci mai tsanani ga gwamnatin, wanda kawai yaren karfi ta ke fahimta".