23 Mayu 2024 - 11:31
Bidiyoyin Yadda Ake Ta Gudanar Da Rakiya Da Juyayin Shahadar Shugaban Kasar Iran Da Abokan Tafiyarsa A Birnin Mashhad

Ambaliyar Miliyoyin Mutane Wajen Taron Juyayin Shahadar Shugaban Kasar Iran Da Ke Gudana Yanzu A Birnin Mashhad Iran

Birnin Mashhad na cikin tunbatsar kuma nan da 'yan mintoci kadan za a gudanar da jana'izar shahidan hidima a birnin Mashhad.

Shahidai na hidima sun kasance cikin da'irar miliyoyin mutanen Mashad anai masu rakiya.

Birnin Mashhad ya dauki baƙi a yau kowa ya zo ya tarbi wannan bawan Allah mai yiwa jama'a hidima. Idanu suna ta kallon hanyar da matafiyan da suka rayu domin wadannan mutane har ta kai ga sun yi shahada saboda kaunar al'ummar da kasarsu.

Yadda saman Birnin Mashhad ta kasance na mutanen Mashhad da suka halarci jana'izar shahidan hidima da ba a taba ganin irinsa ba.

Ambaliyar Miliyoyin Mutane Wajen Taron Juyayin Shahadar Shugaban Kasar Iran Da Ke Gudana Yanzu A Birnin Mashhad Iran yan sa'o'i kadan kafin fara taron jana'izar shahidan hidima a Mashhad mai tsarki.