23 Mayu 2024 - 10:55
Ƙungiyar Gwagwarmaya Ta Nujaba'a Irak Za Ta Gudanar Da Taron Tunawa Da Shahid Ayatullah Raisi + Fosta

Za a gudanar da taron tunawa da shahidai Ayatullah Raisi a birnin Bagadaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: za a gudanar da taron tunawa da shahidan hidima Ayatullah Sayyid Ebrahim Raisi abokin shahadarsa a birnin Bagadaza na kasar Iraki.

Za a gudanar da wannan taron ne tare da halartar Muhammad Kazim Al-Sadiq, jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Iraki.

Za a gudanar da taron ne a ranar Asabar 25 ga watan Mayu 2024 da karfe 16:00 zuwa 19:00 agogon kasar a masallacin Al-Khudiri da ke yankin Al-Arasat a Bagadaza babban birnin kasar Iraki.

Ya kamata a lura da cewa a yammacin ranar Lahadi 19 ga watan Mayun shekara ta 2024 Ayatullah Raisi shugaban jamhuriyar Musulunci ta Iran na takwas a kan hanyarsa ta dawowa daga bikin bude madatsar ruwa ta "Qiz Qalasi" zuwa birnin Tabriz. a yankin Varzghan da ke gabashin lardin Azarbaijan, ya yi hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu, kuma shi da abokansa su kai yi shahada gaba dayansu.

.........