Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Shugaban Ustan Quds Razawi a ganawarsa da iyalan shahid ministan harkokin wajen kasar Iran:
Shahid Amir Abdullahian, ta hanyar kafa kungiyar aiki ta Imam Riza (AS) a ma’aikatar harkokin wajen kasar, ya samar da wata sadarwar alaka tsakanin haramin Imam Rida (AS) da masoyan wannan Imam Rauf a duk fadin duniya, wanda kuma Sayyid Imam Ridha (A) hujjar Allah Ta'ala na takwas ga bayinsa ya ba shi ladan wannan hidima da lambar girma ta shahada.
Wannan kungiyar aiki za ta samar da dimbin Alkhairai da albarka ga maziyarta kasashen waje na Imam Rida (AS); Har zuwa karshen rayuwata zan kasance mai yin addu’a gare shi saboda wannan dinbin hidimar da a yi wa kungiyar da kuma masu ziyarar Haramin Imam Ridha As.